Dubu ta cika: Kwastam ta kwace jarkoki 1,000 makare da man fetur za'a kaiwa yan bindiga a Katsina

Dubu ta cika: Kwastam ta kwace jarkoki 1,000 makare da man fetur za'a kaiwa yan bindiga a Katsina

  • Hukumar kwastam NCS ta bayyana cewa ta samu nasarar kwace jarkokin man fetur sama da 1,000 da ake kaiwa yan bindiga a jihar Katsina
  • Mukaddashin shugaban NCS reshen Katsina, Wada Chide, yace mutane na amfani da abun hawansu wajen siyo fetur su juye a jarkokin
  • Ya kuma yi kira ga mazauna jihar musamman waɗanda ke zaune a kauyukan dake bakin boda su cigaba da kiyaye doka

Katsina - Hukumar kwastam ta ƙasa (NCS) reshen jihar Katsina ta kwace jarkokin man fetur sama da 1,000 da ake kaiwa yan bindiga cikin jeji, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Mukaddashin shugaban NCS reshen jihar, Wada Chide, shine ya bayyana haka a wurin taron al'umma da hukumar ta saba shiryawa don bayyana wa mutane halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Wani Ibtila'i Ya Afkawa Mahalarta Taron Maulidin Annabi SAW a Sokoto, Sama da Mutum 10 Sun Rasu

Chide ya ƙara da cewar hukumar NCS tana haɗa kai da sauran hukumomin tsaro wajen tabbatar da doka da oda a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Jarkokin man fetur
Dubu ta cika: Kwastam ta kwace jarkoki 1,000 makare da man fetur za'a kaiwa yan bindiga a Katsina Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Hannun wa aka kwace jarkokin man fetur?

Mista Chide yace NCS na iyakar bakin kokarinta musamman a wannan lokacin da gwamnati ta ɗauki makamai a koƙarinta na daƙile ayyukan yan bindiga.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Chide yace:

"Sama da jarkokin man fetur 1,000 muka kwace daga hannun mutane, waɗanda suke juye man da suka siyo daga babur zuwa cikin jarkokin. Hakanan kuma mun kwato mashin na hawa kusan 14."
"Mun kwato miyagun kwayoyi waɗanda darajarsu zata kai ta miliyoyin nairori tun da aka kafa sabbin dokoki."

Nawa NCS take tarawa gwamnati na kuɗin shiga?

Da yake jawabi kan harajin da hukumar kwastam ke tarawa gwamnati a dukkan matakai, Chide ya roki mutanen dake zaune a bakin boda su kasance masu biyayya ga dokar ƙasa.

Kara karanta wannan

Bayan Goyon Bayan Gwamna APC, Sabbin Bayanai Sun Fito Kan Yuwuwar Wike Ya Fice PDP

Ya bayyana cewa daga 5 ga watan Satumba zuwa 8 ga watan Oktoba, jami'an kwastam sun kwace kayayyaki na kimanin N50,665,860.

A wani labarin kuma Miyagun yan bindiga sun bude wa masallata wuta, Sun kashe aƙalla 10 a jihar Katsina

Rahotanni sun nuna cewa aƙalla masallata 10 aka kashe yayin da wasu miyagun yan bindiga suka shiga ƙauyen Yasore, ƙaramar hukumar Batsari, jihar Katsina.

Dailytrust ta rahoto cewa lamarin ya auku ne lokacin da mutanen ke tsaka da sallar Magrib ba zato yan bindigan suka buɗe musu wuta, ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262