‘Yan Bindiga Sun Halaka Dan Sanda Da Wasu 22 Sannan Suka Kona Gidaje 50 A Wata Jahar Arewa

‘Yan Bindiga Sun Halaka Dan Sanda Da Wasu 22 Sannan Suka Kona Gidaje 50 A Wata Jahar Arewa

  • Tsagerun yan bindiga sun farmaki garin Gbeji da ke karamar hukumar Ukum ta jihar Benue a ranar Laraba
  • 'Yan bindigar sun halaka mutum 22 da jami'in dan sanda daya sannan suka kona gidaje 50
  • Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce an tura tawagar tsaro don dawo da zaman lafiya

Benue - ‘Yan bindiga sun halaka mutum 23 ciki harda wani jami’in dan sanda sannan suka jikkata mutum 11 yayin da suka kai farmaki garin Gbeji da ke karamar hukumar Ukum ta jihar Benue.

Maharan sun kai mummunan harin ne a ranar Laraba, 19 ga watan Oktoba, jaridar Leadership ta rahoto.

Mai ba gwamnan jihar shawara ta musamman kan harkokin tsaro, Lt Col. Paul Hembah (rtd), wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce dan sandan wanda ya ji mummunan rauni ya mutu ne a hanyar zuwa asibiti.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Farmaki Wani Gari A Zamfara, Sun Kashe Mutum Daya Da Sace Wasu 8

Yan bindiga
‘Yan Bindiga Sun Halaka Dan Sanda Da Wasu 22 Sannan Suka Kona Gidaje 50 A Wata Jahar Arewa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Da yake tabbatar da kashe-kashen, kwamishinan yan sandan jihar, CP Wale Abass, a wata hira ya ce makiyaya biyar sun mutu a harin tare da dan sandan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an tura tawagar yan sanda tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro zuwa yankin don dawo da zaman lafiya.

Wani mazaunin garin wanda ya bayyana sunansa a matsayin Elder Iorngaem Kerepe ya ce baya ga mutanen da aka kashe maharan sun kona akalla gidaje 50.

Ya ce tuni mazauna kauyen suka yi kaura daga gidajensu yana mai cewa har yanzu ba a ga wasu da dama ba.

Ya ce:

“Na kadu da harin, duba ga cewar akwai jami’an sojoji a Kente, wani matsuguni a iyakar Benue-Taraba, kilomita 2 daga Gbeji, da kuma wata tashar bincike na sojoji a Gou, kilomita 3 daga Beji amma makiyaya dauke da makami suka kaddamar da hari tsawon awa daya ba tare da tangarda ba.”

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kutsa Har Cikin Gida Sun Kashe Basarake da Wasu 2 a Jihar Arewa

Har ila yau da yake tabbatar da lamarin, shugaban yankin, Tyoumbur Kaatyo, ya bayyana harin a matsayin wanda bai dace ba yana mai cewa tuni aka ajiye gawarwaki wadanda suka mutu a dakin ajiyar gawa.

Ya kuma ce an kwashi wadanda aka sassara zuwa wani asibitin gwamnati da ke Afia domin samun kulawar likitoci.

Mai ba da shawarar kan tsaro ya bayyana sunayen mutanen da lamarin ya ritsa da su a matsayin Mtem Torpav, Eje Abraham (dan sanda), Zege, Afam Abama, Akor Jem, John Nor.

Sauran sune; Torlumun Orabende, Orpandega Terseer, Bem Nyichia, Atseva Ortwer, Misis Torsar, Nyave Tyoulugh, Kpaver Tion, Ugba Joseph, Mbakumbur Peter, Moses Pav, Apeseza Baba da Unduun, rahoton New Telegraph.

An Samu Tashin Hankali A Shahhararriyar Kasuwar 'Alaba International', Mutane Da Dama Sun Jikkata

A wani labarin, an samu gagarumin tashin hankali a shahararriyar kasuwar nan ta 'Alaba International’ da ke yankin Ojo ta jihar Lagas a ranar Laraba, 19 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Daba' Sun Kai Hari A Wurin Taron Kamfen Din Atiku A Kaduna

Jaridar PM News ta rahoto cewa wasu daruruwan bata gari ne suka yi bata-kashi da yan kasuwa a cikin kasuwar.

An tattaro cewa yan kasuwa sun rufe shagunansu yayin da hankalin mutane ya tashi a cikin kasuwar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel