Dantata: Jerin Mutanen da Suka Mutu a Wasu Kasashe aka Birne Su a Madina
- Birne Aminu Alhassan Dantata a kasa mai tsarki ya sanya mutane waiwaye ga tarihi domin duba mutanen da aka kai su Madina bayan rasuwarsu a wata kasa
- An birne fitaccen attajirin Najeriya, Alhaji Aminu Dantata a makabartar Baƙi'a da ke Madina bayan rasuwarsa a Hadaddiyar Daular Larabawa
- Tsohon shugaban Tunisiya, Ben Ali, da kuma Muhammad al-Badr daga Yemen, su ma an birne su a ƙasa mai tsarki ta Madina bayan rasuwarsu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Madina, ƙasa mai tsarki ga Musulmai, tana da tarin tarihi da ɗaukaka saboda kasancewar birnin da Manzon Allah (SAW) ya rayu kuma aka birne shi.
A dalilin haka, wasu fitattun mutane daga kasashen duniya suna buƙatar a birne su a can bayan mutuwarsu, musamman waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen hidimar addini da jama'a.

Asali: Facebook
A wannan rahoton, mun kawo muku jerin mutanen da suka mutu a ƙasashen ƙetare amma aka ɗauki gawarsu zuwa Madina don a birne su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Dantata ya cika burin birne shi a Madina
Aminu Dantata, fitaccen ɗan kasuwa kuma ɗan ƙasa mai kima daga Najeriya, ya rasu a ranar Asabar a birnin Abu Dhabi na UAE yana da shekaru 94.
Bayan samun amincewar gwamnatin Saudiyya, an ɗauko gawarsa zuwa Madina inda aka yi masa salla a masallacin Annabi kafin a birne shi a maƙabartar Baƙi’a.
BBC ta wallafa cewa Alhaji Dantata ya bar mata uku, 'ya'ya 21 da jikoki 121 kuma jigo ne a harkokin kasuwanci da jin kai.

Asali: Twitter
A shekarar da ta gabata, Aminu Dantata ya ba da Naira biliyan 1.5 ga wadanda ambaliya ta shafa a jihar Borno.
2. An birne Al-Badr na Yemen a Madina
Wani shugaba daga Yemen, Muhammad al-Badr ya samu darajar birne shi a Madina bayan rasuwarsa a London a shekarar 1996 kamar yadda rahoton Asharq ya tabbatar.
Al-Badr, wanda aka haifa a Hajjah, Yemen a shekarar 1929, ya shahara da kishin addini da kuma karatun ilimin addini.
Ko da yake mulkinsa bai wuce mako guda ba a shekarar 1962 kafin ya fuskanci juyin mulki, an girmama shi har zuwa mutuwarsa.
Jaridar Indepedent ta wallafa cewa Al-Badr ya bar 'ya'ya maza biyu, mata biyu a lokacin da ya rasu a ranar 6 ga Agustan 1996 a London.

Asali: Getty Images
3. An birne Ben Ali na Tunisiya a Madina
Tsohon shugaban Tunisiya da ya mulki ƙasar daga 1987 zuwa 2011, Zine El Abidine Ben Ali ya rasu a Saudiyya bayan ya gudu daga kasarsa sakamakon bore da rikice-rikicen da suka faru.
France 24 ta ce Ben Ali ya rasu ne a Saudiyya ba a wata kasa ba, amma an dauko gawarsa daga Jiddah zuwa makabartar Baƙi’a a Madina, kusa da masallacin Annabi Muhammadu (SAW).
Mutuwar wani matashi mai sayar da kaya a shekarar 2010 a Sidi Bouzid ya tayar da bore wanda ya kai ga Ben Ali gudu zuwa Saudiyya, inda ya yi zaman gudun hijira har ya rasu.

Asali: Getty Images
Hukuncin kai gawa zuwa Madina a Musulunci
A wani rahoton, kun ji cewa wani malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Aliyu Muhammad Sani ya yi bayani kan hukuncin kai gawa zuwa kasa mai tsarki.
A jawabin da ya yi, malamin ya ce babu laifi a Musulunci a kai gawa zuwa kasa mai tsarki kamar Madina ko Makka.
Sheikh Aliyu ya kara da cewa malamai sun tabbatar da hakan musamman lura da Annabi Musa (AS) ya nemi a kai gawarsa Kudus domin masa jana'iza.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng