2Baba: Fitaccen Mawakin Najeriya Ya Saki Matarsa, Ya Yi Karin Bayani a cikin Bidiyo

2Baba: Fitaccen Mawakin Najeriya Ya Saki Matarsa, Ya Yi Karin Bayani a cikin Bidiyo

  • Fitaccen mawakin Najeriya, Innocent Idibia (2Baba), ya saki matarsa, jaruma Annie Idibia, bayan zaman aurensu na shekaru 12
  • Bayan wallafa sakon sakin, mawakin ya goge shi daga shafinsa amma daga baya ya yi bidiyo don tabbatar da mutuwar auren
  • Ya zuwa yanzu, tsofaffin ma’auratan sun daina bibiyar juna a shafukan sada zumunta, wanda ke kara tabbatar da cewa sun rabu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Fitaccen mawakin Najeriya, Innocent Idibia, wanda aka fi sani da 2Baba ko kuma Tuface, ya sanar da rabuwa da matarsa, Annie Idibia.

Annie da Tuface sun yi aure a shekarar 2012, wanda ya zama babban biki da aka gudanar na mawaki a lokacin, inda a yanzu suke da 'ya'ya biyu.

Mawaki 2Baba ya tabbatar da sakin matarsa Annie Idibia
Fitaccen mawaki, 2Baba ya sanar da mutuwar aurensa, ya yi karin bayani kan rabuwa da Annie. Hoto: official2baba
Asali: UGC

Mawaki 2Baba ya saki matarsa Annie

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, mawakin da ya yi wakar 'African Queen' ya ce ya saki matarsa 'yan kwanakin da suka wuce.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai jaridar BBC ta rahoto cewa mawaki 2Baba ya goge wannan sako da ya wallafa a Instagram, sannan ya saki bidiyo don tabbatar da sakin.

Sanarwar mutuwar auren mawakin ya tayar da hazo musamman a soshiyal midiya kasancewar sun sha fuskantar kalubale a baya.

2Baba ya warware rudani a cikin bidiyo

Tsohon mamba a tawagar mawakan Plantashun Boyz ya ce zai gudanar da taron manema labarai domin bayar da karin bayani.

"Ni da Annie Macauley sun rabu tun da jimawa, kuma yanzu haka muna cike takardun sakin," a cewar sakon da ya wallafa a Instagram.

Abin mamaki, sai aka ga an goge wannan sakon bayan 'yan mintuna, sannan aka wallafa wani sakon cewa an yi kutse a shafin ne.

Amma mawaki 2Baba ya fito ya yi bidiyo kai tsaye a shafinsa na Instagram, inda ya tabbatar da cewa ya saki matarsa, kuma ba a yi kutse a shafinsa ba.

Kara karanta wannan

"Ana saye ra'ayin 'yan adawa da N50m": Atiku ya tona asirin gwamnatin Tinubu

"Ba ayi kutse a shafina ba, na fadi abin da na fada, amma na zo ne cikin salama."

- 2Baba ya fada a cikin bidiyon.

Inda mawaki 2Baba ya hadu da jaruma Annie

Ya zuwa yanzu dai tsofaffin ma'auratan sun daina bibiyar juna a shafukan sada zumunta, wanda ya kara tabbatar da mutuwar aurensu.

A cikin bidiyon wakarsa da ta yi suna, African Queen, Annie ce ta taka rawa a matsayin jarumar cikin wakar, lamarin da ya sa wasu ke tunanin daga nan suka fara soyayya.

Annie, ta kasance jaruma wacce ta yi suna a soshiyal midiya musamman bayan da ta yi magana kan aurenta da yadda take fama da 'yan matan mijinta.

Kalli bidiyon jawabin 2Baba da shafin Lindaikeji ya wallafa a kasa:

"Na daina dirkawa mata ciki" - 2Baba

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen mawakin Najeriya, Innocent Idibia, da aka fi sani da 2Baba, ya ce ya tuba daga yi wa mata cikin shege.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta yayin bikin Idoma International Carnival.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu kan bidiyon, la’akari da cewa yana da ‘yan mata akalla uku da suka haifa masa yara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.