Mawakin Najeriya 2Baba zai yi takarar wata kujera a zabe mai zuwa

Mawakin Najeriya 2Baba zai yi takarar wata kujera a zabe mai zuwa

- Shararren Mawakin nan 2Baba yace zai fito takarar ofis a zabe mai zuwa

- Mawakin yace idan ya samu mukami zai yi gaskiya ya kuma rike amana

- Babban Mawakin yace ya kamata mutanen kwarai su shiga harkar siyasa

Babban Mawakin nan na kasar nan da yayi fice tun a da watau Innocent Idibia wanda aka fi sani da 2Baba ya bayyana cewa da shi za ayi takara a zabe mai zuwa na 2019 domin gyara kasar nan.

Innocent Idibia yayi hira da ‘Yan jarida a makon nan inda ya tabbatar masu da cewa zai yi takara a Najeriya domin ganin ya fitar da jama’a daga cikin halin kunci da su ka shiga. 2Baba dai bai bayyana ofishin da ya ke hari ba.

KU KARANTA: Bai halatta su Saraki su sauya-sheka ba inji wani Lauya

Mawakin yace idan har ya samu dama zai yi gaskiya tare da rike amanar jama’a a matakin sa. Mawakin yayi kira ga sauran mutanen kirki su shigo cikin harkar siyasa domin a ceci kasar nan daga kangin da ake ciki a halin yanzu.

2Baba dai ya nuna cewa halin da mutanen kasar nan ke ciki yana matukar damun sa don haka yake neman ganin yayi wani abu. Mawakin ya koka game da kashe-kashen da ake yi a kasar musamman a Jihar sa ta Benuwai.

Kun san cewa dai an kashe mutane da dama a Benuwai don haka fitaccen Mawakin yake neman jama’a su kawo masu dauki da gudumuwa. Mawakin yace ba a Mahaifar ta sa kadai ake fama da irin wannan matsala a cikin Najeriya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng