Nigerian news All categories All tags
Tuface zai fito takara kuma ya nemi Shugaba Buhari ya kawo karshen rikicin Makiyaya

Tuface zai fito takara kuma ya nemi Shugaba Buhari ya kawo karshen rikicin Makiyaya

- Tuface yayi kira ga Jama’a su shiga harkar siyasa domin su kawo gyara

- Mawakin ya kuma yi tir da rikicin da ke aukuwa a irin su Jihar Benuwe

- Babban Tauraron yace lokaci yayi fa da mutanen kirki za su shiga siyasa

Babban Mawakin Afrika Innocent Idibia wanda aka fi sani da Tuface ya bayyana cewa yana shirin shiga harkar siyasa a Najeriya domin ya kamata a rika damawa da na-gari inji Mawakin ya kuma nemi a kawo karshen rikicin Makiyaya.

Tuface zai fito takara kuma ya nemi Shugaba Buhari ya kawo karshen rikicin Makiyaya

Tuface ‘Dan asalin Jihar Benuwe yace rikici ya dabaibaye Najeriya

Tuface a wani taro da aka yi kwanan nan a Legas ya bayyana cewa lokaci yayi da mutanen da su ka san abin da ya dace za su shiga harkar siyasa. Mista Idibia yace burin sa ya taimakawa jama’a inda yayi kira ga matasa su tashi tsaye.

KU KARANTA: An kama Jami'an tsaro da laifin sata da fashi da makami

Bayan Mawakin ya nemi Matasan su shiga harkar siyasa, ya sanar da cewa zai shiga cikin wata Jam’iyya domin a dama da shi. Fitaccen Mawakin yace yana rokon Ubangiji ya kawo ranar da na-gari za su gyara kasar nan a ji dadi.

Mawakin ya nuna cewa siyasa ita ce rayuwar jama’a don haka dole a shiga domin a kawo gyara. 2 Face kuma nemi a rika agazawa wanda rikicin Makiyaya da manoma ya fada kan su ya kuma yi kira Gwamnatin Tarayya ta dauki mataki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel