Bauchi: Ana Kukan Rashin Ruwa, Gidauniya Ta Kawo Mafita, Ta ba Mata Danƙareren Gida
- Wasu yankuna a Bauchi ta Kudu sun yi murna da Gidauniyar Ibrahim Ali Usman ta gyara rijiyoyi 100 domin magance matsalar ruwan sha
- Gidauniyar ta kuma tallafa wa wata mata mai suna Barakatu, inda ta gina mata gida bayan rushewar gidan da take zaune a ciki
- Barakatu ta nuna godiyarta ga Hon. Ibrahim Ali Usman ta hanyar ba shi Alkur'ani mai girma tare da yin addu'oi na musamman gare shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Bauchi - Wasu yankunan Bauchi ta Kudu sun barke da murna bayan Gidauniya ta gyara musu bohula har guda 100 a kananan hukumomi bakwai.
Gidauniyar Hon. Ibrahim Ali Usman ta gyara akalla rijiyoyi 100 a shiyar Bauchi ta Kudu domin rage wa al'umma wahalhalu ta bangaren ruwan sha.

Asali: UGC
Gidauniyar Ibrahim Ali Usman ta raba littattafai
Daraktan yada labaran Gidauniyar, Nuruddeen Yakubu Haske shi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa a yau Litinin 20 ga watan Janairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan Gidauniyar Hon. Ibrahim Ali Usman ta tallafawa ɗalibai da littattafai domin inganta harkokin ilimi a jihar Bauchi da ke Arewacin Najeriya.
Gidauniyar ta ƙaddamar da tallafin litattafai akalla guda miliyan daya domin tallafa wa ɗaliban Bauchi ta Kudu a wani babban taro da aka gudanar.
Shugaban Gidauniyar, Hon. Ibrahim Ali Usman ya bayyana cewa 'Ibrahim Ali Usman Foundation' za ta ci gaba da tallafawa ilimi a jihar musamman mata da yara.
Kungiyoyi da dama sun karrama Hon. Ibrahim Ali Usman bisa gudunmawar da yake bayarwa kamar yadda mai magana da yawun Gidauniyar ya fadawa Legit Hausa a makon jiya.
Gidauniya ta gyara rijiyoyi 100 domin al'ummar Bauchi
Daraktan yada labaranta, Nuruddeen Yakubu Haske ya ce Gidauniyar ta kuma gina wa wata mata mai suna Barakatu gida a Unguwar Makafi da ke Bauchi.
Hakan ya biyo bayan rushewar gidan matar da ya yi wanda Gidauniyar ta tausaya mata tare da tallafa mata da dankareren gida.
"Gidauniyar Ibrahim Ali Usman ta gyara rijiyoyi 100 a shiyyar Bauchi ta Kudu, ta kuma gina kyautar gida ga Barakatu a Anguwan Makafi, Bauchi."
- Nuruddeen Yakubu Haske
Mata ta yi godiya bayan ba ta gida
Yayin da take godiya a cikin wani faifan bidiyo, Barakatu ta zubar da hawaye inda ta yi wa Hon. Ibrahim Ali Usman addu'oi na musamman.
Daga bisani, Barakatu ta ba Hon. Ibrahim Ali Usman kyautar Alkur'ani mai girma domin nuna masa jin dadinta kan lamarin.
Gidauniya ta warkar da makafi a Kano
A baya, kun ji cewa wata Gidauniya a jihar Kano ta taimakawa makafi akalla 3,000 da tiyata kyauta domin dawo musu da farin cikinsu a rayuwa.
Gidauniyar karkashin jagorancin Hon. Umar Datti wanda ke wakiltar Kura/Garunmallam/Madobi a Majalisar Tarayya ta yi hakan ne domin taimakon marasa ƙarfi.

Kara karanta wannan
Abin da Kashim Shettima ya ce kan bikin Maulidi a Kano duk da zargin kokarin hana taron
Al'ummar da wannan tallafi ya shafa sun yi godiya ga Gidauniyar da kuma dan Majalisar inda suka kwarara masa addu'o'i ma musamman da fatan alheri a rayuwarsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng