Gwamna Bala Muhammad ya nada hukumar gudanarwar a ma’aikatar ruwan sha ta Bauchi

Gwamna Bala Muhammad ya nada hukumar gudanarwar a ma’aikatar ruwan sha ta Bauchi

-Gwamnan jihar Bauchi ya nada hukumar gudanarwar ma'aikatar ruwan sha ta Bauchi domin magance matsalar ruwan sha a jihar

-Kakakin gwamnan, Dakta Ladan Salihu ne ya bada wannan sanarwa a ranar Laraba 3 ga watan Yulin 2019

-A cikin zancen kakakin ya bayyana sunan shugaban jam'iyyar PDP na jihar Bauchi a matsayin wanda zai jagoranci hukumar ta gudanarwa

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammad a ranar Laraba ya aminta da nadin hukumar gudanarwa wacce zata kula da lamuran ma’aikatar samar da ruwan sha ta jihar bauchi domin magance matsalar jihar a bangaren ruwan sha.

An samu labarin wannan sanarwar ne ta hannun kakakin gwamnan, Dakta Ladan Salihu a ranar Laraba 3 ga watan Yuli, 2019.

KU KARANTA:Buhari ya aminta da tsarin ciniki maras shinge na Afirka

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Bauchi, Alhaji Hamza Koshe Akuyam shi ne shugaban hukumar. Yayin da daga cikin mambobin hukumar akwai; Aliyu Aminu Gital, Dakta Musa Lukshi, Usman Aliyu Shira da Garba Aliyu Bagel.

Har ila yau, akwai Alhaji Hafiz Umar Mai’Auduga da kuma Misis Lydia Shehu. Zancen da ya samar da sanarwar ya bada bayanin cewa, gwamnan ya nada wannan hukumar ne a dalilin kawo sauyi a bangaren matsalolin ingantancen ruwan sha dake addabar jihar.

A wani labarin mai kama da wannan, zamu ji cewa gangamin gwamnonin APC sun nuna gogyon bayansu ga tsohon gwamnan jihar Bauchi, M. A Abubakar na a bashi muqamin minista a cikin sabbin ministocin da Buhari zai nada kwanan nan.

Gwamnonin sun ba shi goyon baya ne, bisa namijin kokarin da ya yi a zaben da aka gudanar a wannan shekara na shugaban kasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng