Bauchi: Gidauniya Ta Raba Littattafai Miliyan 1 Saboda Inganta Ilimi, an Yaba Mata
- Gidauniyar Ibrahim Ali Usman ta tallafawa ɗalibai da littattafai domin inganta harkokin ilimi a jihar Bauchi da ke Arewacin Najeriya
- Gidauniyar ta ƙaddamar da tallafin litattafai akalla 1,050,000 domin tallafa wa ɗaliban Bauchi ta Kudu a wani babban taro
- Shugaban Gidauniyar, Hon. Ibrahim Ali Usman ya bayyana cewa 'Ibrahim Ali Usman Foundation' za ta cigaba da tallafawa ilimi a jihar musamman mata da yara
- Kungiyoyi da dama sun karrama Hon. Ibrahim Ali Usman bisa gudunmawar da yake bayarwa kamar yadda mai magana da yawun Gidauniyar ya fadawa Legit Hausa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Bauchi - Wata Gidauniya a jihar Bauchi ta ba da tallafin littattafai ga ɗalibai a yankin Bauchi ta Kudu da ke Arewacin Najeriya.
Shugaban Gidauniyar, Hon. Ibrahim Ali Usman ya ƙaddamar da tallafin litattafai guda 1,050,000 ga ɗaliban domin inganta harkokin ilmi.

Asali: Facebook
Gidauniya ta warkar da makafi a Kano
Daraktan yada labaran Gidauniyar, Nuruddeen Yakubu Haske shi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa a yau Alhamis 16 ga watan Janairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gidauniyoyi da dama na taimakon al'umma a bangarori da yawa domin inganta rayuwar mutane da kuma marasa karfi.
A baya, mutane akalla 3,000 suka ci gajiyar Gidauniyar dan Majalisar Tarayya a jihar Kano, Hon. Umar Datti bayan yi musu tiyata kyauta.
Gidauniyar ta taimaki makafi da dama inda ta yi musu aiki kyauta tare da yin nasarar dawo musu da idanunsu.
Gidauniyar karkashin shugabancin Hon. Yusuf Umar Datti ta yi nasarar yi wa mutane 3,000 tiyatar ido ba tare da sun biya ko sisin kwabo ba.
Wadanda suka ci gajiyar sun fito ne daga mazabar dan Majalisar Tarayya, Hon. Datti Kura ta Kura/Garunmallam/Madobi da ke jihar Kano.
Gidauniyar Ibrahim Usman ta tallafa wa dalibai
Yakubu Haske ya fadawa Legit Hausa cewa Gidauniyar tana da niyyar ci gaba da tallafawa ilimi musamman a kananan hukumomin Bauchi ta Kudu.
Ya ce kowace karamar hukuma daga cikin bakwai a Bauchi ta Kudu za ta samu litattafai 150,000 domin ilmantar da yara da inganta rayuwar matasa.

An karrama shugaban Gidauniyar, Hon. Ibrahim Usman
Haka kuma, ya jaddada cewa gidauniyar za ta ci gaba da ayyukan alheri musamman ga mata da yara domin cigaban al'umma.
Daga bisani, ya ce kungiyoyi daban-daban sun karrama Alhaji Ibrahim Ali Usman bisa jajircewarsa a taimakon al'umma, musamman a Bauchi ta Kudu.
Shugaban Gidauniyar, Ibrahim Ali Usman ya roki Allah SWT ya bashi ƙarfi da hikima domin cigaba da ayyukan alheri da ci gaban jihar Bauchi.
An gudanar da addu'o'i ga Gwamna Kefas
A wani labarin, al'ummar Musulmi sun gudanar da addu'o'i na musamman ga Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba.

Kara karanta wannan
Abin da Kashim Shettima ya ce kan bikin Maulidi a Kano duk da zargin kokarin hana taron
An gudanar da addu'o'in ne a ranar Asabar 4 ga Janairun 2025 domin Gwamna Kefas da kuma ci gaban jihar Taraba gaba daya.
Hadimin gwamnan a bangaren harkokin addinin Musulunci ya ce sun taru a masallacin Juma'a na Saurara ne da ke birnin Jalingo domin addu'o'in zaman lafiya.
Asali: Legit.ng