"Na Gaji da Zama Ni Kadai": Dattijuwa Ta Sharbi Kuka a Bidiyo, Tana Neman Mijin Aure Ko Saurayi

"Na Gaji da Zama Ni Kadai": Dattijuwa Ta Sharbi Kuka a Bidiyo, Tana Neman Mijin Aure Ko Saurayi

  • Wata mata ta yi kuka sosai a cikin wani faifan bidiyo, inda ta shaida wa jama'a cewa ta daɗe ba ta da abokin rayuwa
  • Matar ta ce tana neman soyayya tunda ta gaji da zama marar aure kuma ita kaɗai ba tare da masoyi ba
  • Ta ce tana bukatar gaggawar zama matar wani ko akalla budurwa idan ba za ta iya samun miji ba

Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Wata dattijuwar mata ta yi kuka mai zafi a cikin wani faifan bidiyo, tana mai cewa ta daɗe tana rayuwar kaɗaici babu mijin aure.

Ta koka kan yadda ta yi ta ƙoƙarin neman soyayya ba tare da wata nasara ba, inda ta ce hakan ya sa ta ji kaɗaici.

Dattijuwa na neman mijin aure
Dattijuwa na neman mijin aure ko saurayi ido rufe Hoto: @jesuispope
Asali: Twitter

A cikin faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, an ga matar tana zubar da hawaye, tana mai nuna rashin jindaɗinta kan rashin samun miji ko saurayi.

Kara karanta wannan

Budurwa ta cire kunya ta nemi saurayi ya bata lamba, sun kusa aure

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyonta ya sosa zukata sosai

Ta bayyana cewa tana buƙatar masoyi a rayuwarta. Ta ce tana buƙatar wanda zai zama miji ko saurayi a gare ta.

Matar ta ce tana neman soyayya tunda ta gaji da zama marar aure kuma ita kaɗai ba tare da masoyi ba, ta ce tana buƙatar zama matar wani ko akalla budurwa idan ba za ta iya samun miji ba.

Hawayenta sun sosa zukatan masu amfani da yanar gizo da dama, wasu sun tausaya mata tare da yi mata addu'ar samun abokim soyayya da wuri.

An sanya bidiyon ne dai a shafin Twitter na @jesuispope

Kalli bidiyon a nan ƙasa:

Wane martani ƴan soshiyal midiya suka yi?

@OrAcle4romThaO ya rubuta:

"Abu ɗaya da babu wanda zai iya kauce masa shi shine shekaru!"

@unclescholes123 ya rubuta:

Kara karanta wannan

"Ina da bidiyo" Sanata ta tona asirin gwamnan arewa, ta faɗi yadda ya yi yunƙurin kashe ta

"Kai!!! Wannan gaskiya ne, Allah ya ƙara mata kwanciyar hankali, ya kuma kawo mata nagari hanyarta, abinda wasu matan suke wasa da shi, shi ne wata ke nema ido rufe."

@official_adags ya rubuta:

"Tabbas ta cancanci farin ciki, don Allah wani ya taimaka mata kafin ta shiga damuwa."

@betty_nwabunike ta rubuta:

"Gaskiya ina fatan ba mijin aure kaɗai za ki samu ba, amma mijin nagari wanda zai kyautata miki."

Budurwa Na Neman Mijin Aure

A wani labarin kuma, wata kyakkyawar budurwa ta garzaya shafin yanar tana neman wanda zai aureta su yi rayuwar miji da mata.

Budurwar ta bayyana cewa tana da sharuɗa wanda daga ciki shi ne sai dole wanda yake son ya aureta yana kwasar albashin N300k a kowane wata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel