Budurwa Ta Cire Kunya Ta Nemi Saurayi Ya Bata Lamba, Sun Kusa Aure

Budurwa Ta Cire Kunya Ta Nemi Saurayi Ya Bata Lamba, Sun Kusa Aure

  • Wata yar TikTok ta ba da labarin yadda ta kulla alaka da mai shirin aurenta ta hanyar tambayar lambar wayarsa
  • Matar ta bayyana cewa duk da kasancewar ita ce ta fara tunkararsa, alakarsu cike take da so da mutuntawa
  • Bidiyon ya kuma nuna lokacin da ya nemi ta aure shi kuma ta amsa, wanda ke nuna soyayyarsu hadin Allah ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata mata ta garzaya dandalin TikTok don bayar da labari mai ban al'ajabi na yadda ta hadu da mai shirin zama mijinta da yadda ya nemi aurenta cike da shauki.

Wata mata mai suna @i_am_evelyn, ta bayyana cewa ita ce ta fara nuna tana ciki a lokacin da ta yi arba da shi sannan daga bisani ta nemi ya bata lambar wayarsa.

Kara karanta wannan

Wani fasto mai tsala-tsalan mata 2 kuma yake shirin auren ta 3 ya hakura, ya fadi dalili

Saurayi da budurwa
“Girman Kai Ba Zai Barni Ba”: Budurwa Ta Nemi Saurayi Ya Bata Lambar Wayarsa, Sun Kusa Aure Yanzu Hoto: TikTok/@i_am_evelyn
Asali: TikTok

Ta kara da cewar duk da kasancewar ita ta hada soyayyar, alakarsu na cike da so, yarda da goyon bayan junansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun kasance tare tsawon shekaru biyu kuma basu taba kallon baya ba. Bidiyon ya kuma nuna lokacin da ya duka don neman aurenta, yayin da yake rike da zobe mai dan karan kyau.

Ta amsa bukatarsa cike da farin ciki sannan ta rungume shi, yayin da abokansu ke taya su murna.

Bidiyon ya yadu a TikTok inda dubban mutane suka kalla da yin sharhi tare da jinjinawa soyayyarsu da yi masu fatan alkhairi.

Mutane da dama sun kuma jinjinawa karfin gwiwar matar ta yadda har ta fara tunkararsa, sannan sun ce wanka ya biya kudin sabulu.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan bidiyon masoya

Kelly ya ce:

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: Matar aure ta haifi tagwaye kasa da awanni 24 bayan mutuwar mijinta

"Don Allah kada wanda ya tambayi lamba na, rayuwa ta yi wahala.

Qwinlaura312 ta rubuta:

"Sai dai na ji sha'awar gaye daga nesa ba zan taba tunkararsu sannan na tambayesu lamba ba."

Nurse Mimi:

"Ta yaya kika fara wannan yunkuri."

Iris stitches:

"Girman kai ba zai bar ni ba, ina fatan ba zan mutu ba tare da aure ba."

Fasto ya hakura da aure na uku

A wani labarin, wani faston kasar Botswana mai suna Sekati Kemmonye, ya canja shawara game da shirinsa na auren mata ta uku.

A wata wallafa da ya yi a shafin Facebook a ranar Talata, 31 ga watan Oktoba, Fasto Sekati ya bayyana cewa ya gama auren sannan ya ba yan matan da ke muradin zama matansa ta uku da su yi hakuri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel