Kyakkyawar Budurwa Na Neman Mijin Aure, Ta Bayyan Irin Wanda Take Son Samu

Kyakkyawar Budurwa Na Neman Mijin Aure, Ta Bayyan Irin Wanda Take Son Samu

  • Wata matashiyar budurwa ta janyo cece-kuce bayan ta bayyana irin namijin da take so wanda zai aureta
  • A wani rubutu da aka sanya a Twitter, budurwar ta lissafo wasu sharuɗɗa da namijin zai cika kafin su fara soyayya
  • Ɗaya daga cikin sharuɗɗan na ta shi ne dole ne sai wanda ya ke sonta ya kasance mai arziƙi wanda bai samun kasa da N300k a wata

Wani mai amfani da sunan @Abu_jawaadd a Twitter, ya sanya hoton wani saƙo da wata budurwa mai neman mijin aure ta turo masa.

Budurwar dai tana matuƙar buƙatar neman mijin aure wanda yake ɗaukar albashin N300,000 ko fiye da haka a wata.

Kyakkyawar budurwa na neman wanda za ta aura
Kyakkyawar budurwa na neman mijin aure Hoto: The Good Brigade/ Getty Images. Hoton an yi amfani da shi ne kawai domin misali
Asali: Getty Images

Ya rubuta a jikin hoton cewa:

"Wata ƴar uwa tana neman mijin aure amma sai albashinka ya kai N300k ko fiye da haka."

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku Ya Fadi Iya Wa'adin Da Ya Ragewa Bola Tinubu a Kan Kujerar Shugabanci, Ya Ba Shi Shawara

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Saƙon wacce budurwar mai suna Bilkisu ta turo, ya bayyana irin kalar mijin da take son samu.

Ta bayyana cewa shekarunta 25 a duniya, Bahaushiya, mai ƙiba, ɗalibar jami'a mai karantar 'Microbiology' sannan ƙwayun halittarta AA ne.

Irin mijin da budurwar ke son samu

Bilkisu ta bayyana cewa tana son samun kyakkyawan saurayi mai shekaru 28 zuwa 35, mai albashin da bai gaza N300,000, mai mota sannan wanda ya fito daga gidan mutunci.

Haka kuma, ta nuna muhimmanci kan karatu, wayewa da iya Turanci da Larabci.

Bilkisu ta bayyana cewa wanda take son samun dole ne ya kasance mazaunin Kano, Kaduna ko Abuja.

A kalamanta:

"Barka, sunana Bilkisu ƴar shekara 25, Bahaushiya, mai ƙiba, mai yin karatun digiri a kan (microbiology), ƙwayar halitta AA, daga jihar Kano."

Kara karanta wannan

Kasar Faransa Ta Haramta Dalibai Musulmai Sanya Hijabi a Makarantu

"Ina son samun kyakkyawan saurayi wanda bai wuce shekara 28 zuwa 35 ba, wanda albashinsa bai gaza N300k ba, mai mota wanda ya fito daga gidan mutunci."
"Dole ne ya kasance ya yi karatu, wayayye kuma ya iya Turanci da Larabci. Dole ne ya kasance mazaunin Kano, Kaduna ko Abuja. Nagode."

Martanin ƴan soshiyal midiya kan buƙatun Bilkisu

Abubuwan da Bilkisu ta zayyano dai sun janyo cece-kuce a soshiyal midiya. Da yawa daga cikin waɗanda suka yi sharhi, sun nuna cewa ta cika buri da yawa.

@_Nwanneamaka ta rubuta:

"To menene abin dariya idan tana son mai albashin N300k ko fiye da haka?"

@HamzatMusaOpey1 ya rubuta:

"Ku ba ta ƙasa kawai ta gina shi da kanta."

@Saifullah ya rubuta:

"Menene albashin mahaifinta?"

@lamHolarlekhan ya rubuta:

"Har yanzu shekarunta 25, kafin ta kai shekara 30 burinta zai cika."

Fasto Ƴa Shawarci Maza Su Kara Aure

A wani labarin kuma, wani fasto ya janyo cece-kuce bayan ya shawarci mazaje da su riƙa auren mata huɗu.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Sake Kai Farmaki a Zariya, Sun Yi Awon Gaba Da Bayin Allah

Fasto Meshack Aboh ya bayyana cewa auren mata da yawa yana sanyawa mutum ya yi tsawancin kwana a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng