Saurayi Ya Tsaya A Cikin Rana Yayin Da Budurwarsa Ta Je Tattaunawa Da Attajiri, Bidiyon Ya Yadu

Saurayi Ya Tsaya A Cikin Rana Yayin Da Budurwarsa Ta Je Tattaunawa Da Attajiri, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani matashi ya burge mutane bayan budurwarsa ta je karbo lambar wayan wani attajiri
  • Saurayin wanda dan Najeriya ne ya na tsaye a cikin rana yayin da budurwar ta je wurin mai motar
  • Mutane sun yabi halin matashin da cewa ya na da fahimtar rayuwa yayin da wasu ke cewa ba shi da tabbas a kanta ne

Abin mamaki yayin da aka gano wani saurayi na jiran budurwarsa ta je karban lambar wayan wani mai mota.

Saurayin na tsaye a rana cikin hakuri yayin da budurwar ta je wurin wani mai mota su na tattaunawa, Legit.ng ta tattaro.

Budurwa ta shanya saurayinta a rana
Yadda Saurayin Ya Tsaya A Rana Ya Na Jiran Budurwarsa. Hoto: @instablog9ja/Instagram.
Asali: Instagram

Meye mutane ke cewa kan faifan bidiyon?

A wani faifan bidiyo, saurayin dan Najeriya ya sha yabo a wurin mutane inda su ke mamakin hakurinshi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da wasu ke caccakar matashin ganin yadda budurwar ta ci mutuncinshi ya na tsaye ya na kallonsu da wani.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Halin da saurayin ya nuna ya tabbatar da muhimmancin hakuri da juriya.

Wasu mutane kuma a bangarensu sun yi zargin ko matashin ba shi da kwarin gwiwa a karan kansa ne.

Martanin jama'a kan bidiyon saurayin da budurwarsa:

@hypeman_lyte:

"Saurayin ya na fahimta, mu na ganin abu da yawa."

@adedoyin.gram:

“Ko ba komai shi ba dan bakin ciki ba ne, kuma ba mai taurin kai ba."

@sharon.chigozirim:

“Kada ki bari saurayinki ya hana ki ganawa da mai aurenki."

@aver nessa:

"Tabbas ya na son ci gabanta, ba shi da bakin ciki."

@iamnaniboi:

“Allah sarki, wannan akwai karfin fahimta."

@sweetest babyyysophie:

“Rayuwa ba wahala, ku kuke daukar hakan da zafi, ya na son ci gabanta"

@anita_dera_:

“Ko da ba na son mutum ba zan masa cin mutuncinshi ba."

Bidiyon Santala-Santalan 'Yan Mata Na Leburanci

A wani labarin, wasu 'yan mata sun ba da mamaki yayin da aka gano su a wani faifan bidiyo su na aikin leburanci.

Kyawawan 'yan matan na kwaba siminti da kuma jidon bulok don kai wa wata da ke gini a gefe.

Mutane da dama sun yabi matan da cewa ba su kashe zuciyarsu kamar saura ba su na tsammani daga samarinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel