Promise Da Terry: Yar Shekara 42 Na Soyayya Da Dan Shekara 22, Hotunansu Sun Kayatar

Promise Da Terry: Yar Shekara 42 Na Soyayya Da Dan Shekara 22, Hotunansu Sun Kayatar

  • Promise da Terry suna matuƙar ƙaunar juna inda suka nunawa masoyansu cewa shekaru ba wani abu ba ne da wuce lamba
  • Terry ƴar ƙasar Kenya ce mai shekara 42 a duniya, Promise mai shekara 22 a duniya yana da tasha a YouTube inda ba ya shakkar nuna masoyiyarsa
  • Terry ta taɓa bayyana cewa ta saya wa masoyin na ta fili inda ta sanya sunansa a ciki saboda ƙaunar da take yi masa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani matashi mai shekara 22 a duniya mai suna Promise da masoyiyarsa Terry mai shekara 42 a duniya sun ɗauki hankula a yanar gizo.

Labarin soyayyar Terry da Promise ya dauki hankula
Promise da Terry na matukar kaunar juna Hoto: Promise_254
Asali: UGC

1. Promise da Terry suna ƙaunar juna

Masoyan biyu sun ɗauki hankula sosai tun bayan da suka bayyana cewa suna soyayya da juna. Abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne Terry ta girmi mahaifiyar masoyinta.

Kara karanta wannan

Shin Da Gaske CBN Na Son Sauya Fasalin Naira Domin Ta Dawo Daidai Da Dala? Bayanai Sun Fito

Matar mai shekara 42 ba ta damu da abin da ƴan gutsiri tsoma ke cewa ba, inda ta yi nuni da cewa tana matuƙar ƙaunar masoyin na ta mai shekara 22.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2.Terry da Promise sun bayyana yadda suka haɗu

Terry ta bayyana cewa masoyin na ta cetonta ya taɓa yi inda daga nan ne labarin soyayyarsu ya fara.

Labarin soyayyarsu ya ba mutane da yawa mamaki inda da dama daga ciki suke shawartar Promise ya nemi budurwa ɗanyen jini.

3. Promise da Terry sun shirya sanya iyaye a soyayyarsu

Masoyan biyu sun bayyana cewa har yanzu ba su ga iyayen juna ba. Sai dai, suna yawan bayyana soyayyarsu a soshiyal midiya.

A TikTok suna yawan sanya bidiyonsu inda suke gargaɗin maƙiya su fita harkar su.

4. Promise da Terry na da tasha a YouTube?

Kara karanta wannan

"Ba Aikin Yi": Dan Najeriya Da Ya Koma Canada Neman Rayuwa Mai Kyau, Ya Tattaro Komatsansa Ya Dawo Gida

Masoyan biyu suna ƙaunar juna inda labarin soyayyarsu suke sanya shi a tashar Youtube ɗin Promise.

5. Promise ya ce Terry ce mace ta farko da ya taɓa ɗora wa a midiya

Matashin mai shekara 22 ya bayyana cewa yana matuƙar ƙaunar Terry. Ya bayyana cewa ita ce mace ta farko da ya taɓa sanya wa a soshiyal midiya.

Terry har fili ta taɓa saya wa Promise inda ta sanya sunansa a ciki.

Dattijuwa Ta Koka Kan Rashin Aure

A wani labarin na daban, wata tsohuwa ta bayyana yadda mahaifinta ya ja mata ta kwashe shekaru masu yawa a duniya ba tare da ta taɓa aure ba.

Tsohuwar mai shekara 95 a duniya ta bayyana cewa duk da shekarun da ta kwashe a duniya, ba ta taɓa yin aure ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel