Budurwa Ta Kamu Da Son Dan Ajinsu, Sun Yi Aure Bayan Shekara 7

Budurwa Ta Kamu Da Son Dan Ajinsu, Sun Yi Aure Bayan Shekara 7

  • Wata budurwa ta auri ɗan ajinsu wanda suka yi soyayya tare shekaru da dama da suka gabata a lokacin da suke makaranta
  • Budurwar ta wallafa wani bidiyo kuma ta bayyana cewa ita da saurayin nata sun kwashe shekara bakwai suna soyayya kafin ya nemi aurenta
  • Bidiyon ya nuna ranar da ya nemi aurenta, sannan ya nuna lokacin da aka yi ƙayataccen bikinsu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata budurwa ta kamu da son ɗan ajinsu lokacin da suke karatu a makaranta, inda daga ƙarshe suka zama miji da mata.

Budurwar mai suna, Nortie Ehlla, ta sanya wani bidiyo akan TikTok domin yi wa mabiyanta ƙarin bayani, bayan an sha shagalin bikinsu ita da mijinta.

Budurwa ta auri dan ajinsu
Budurwa ta auri dan ajinsu bayan shekara 7 suna soyayya Hoto: TikTok/@nortie_ehlla
Asali: TikTok

A cikin faifan bidiyon, Ehlla ta bayyana cewa sun kwashe shekara bakwai suna soyayya, inda ta yi ta haƙuri tana jiran zuwan lokacin da zai fito domin neman aurenta.

Kara karanta wannan

'Ki Na Da Aljanu Ne?" Bayan Shekaru 2, Budurwa Ta Rabu Da Saurayinta Saboda Ba Ya Dukanta, Bayanai Sun Fito

Lokacin da ya nemi ya aurenta, Ehlla ba ta ɓata lokaci ba wajen nuna amincewarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon an nuna lokacin da saurayin ya durƙusa domin ba ta zobe, wanda hakan ya nuna aniyarsa ta son cigaba da kasancewa da ita har zuwa ƙarshen rayuwarsa.

Bidiyon ya kuma nuna ranar ɗaurin aurensu yayin da suke cike da farin cikin kasancewa ma'aurata.

Mutane da dama da suka kalli bidiyon, sun yabawa Ehlla kan haƙurin da ta yi na jiran saurayin nata har na tsawon shekara bakwai.

Ƴan soshiyal midiya sun yi martani

@cypher_dinaris00 ya rubuta:

"Ku nuna mana tsaffin bidiyon ku tare."

@Bake’n’flake ta rubuta:

"Bari na je na karɓi fom ɗin makaranta, mijina yana makaranta."

@yokiejoe956 ta rubuta:

"Babu mijin aure a ƴan ajinmu. Abin da kawai suka sani shi ne ka yi karatu idan an je ɗakin jarabawa ka ba su, su kwashe."

Kara karanta wannan

"Sabuwa Fil a Leda": Ango Ya Nuna Zumudinsa Bayan Ganin Fuskar Amaryarsa a Daren Farko, Bidiyon Ya Yadu

@Og Fokos ta rubuta:

"Idan na yi soyayya da ɗaya daga cikin samarin ajinmu, sauran ba za su yarda su bani kwaki ba."

Budurwa Ta Rabu Da Saurayinta

A wani labarin kuma, wata budurwa ta yanke shawarar rabuwa da saurayinta wansa suka kwashe shekara biyu suna soyayya.

Budurwar ta ɗauki wannan matakin ne bayan saurayin nata ya ƙi yarda ya ci zarafinta a tsawon lokacin da suka kwashe suna soyayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel