Ziyara Zuwa Kano: Shigar Da Jarumar Fim Nancy Isime Ta Yi Ya Bada Mamaki, Ana Ta Tafka Mahawara

Ziyara Zuwa Kano: Shigar Da Jarumar Fim Nancy Isime Ta Yi Ya Bada Mamaki, Ana Ta Tafka Mahawara

  • Fitacciyar jarumar fina-finai na Nollywood, Nancy Isime ta ja hankulan masu amfani da yanar gizo bayan ta wallafa wasu hotunanta a shafin sada zumunta
  • Fitacciyar mai amfani da kafar sadarwar ta ɗora wasu hotuna masu kayatarwa da ta ɗauka a wata ziyara da ta kai arewacin Najeriya
  • Yanayin shigar da jaruma Isime ta yi ne ya haifar da cece-kuce masu rikitarwa, inda har wasu ke tambayar ko ta Musulunta ne

Fitacciyar jarumar fina-finan kudancin Najeriya wato Nollywood, Nancy Isime, ta jawo cece-kuce bayan wallafa wasu sabbin hotuna masu ƙayatarwa a wata ziyarar da ta kai Kano.

Jarumar fina-finan ta yi shiga ta ƙawa irin shigar musulmai, kuma cikin korayen kaya masu ɗaukar hankali da aka ɗinka ma ta su musamman domin ziyarar.

Nancy Isime ta yi kyau sosai cikin koriyar rigar sut ɗinta, da hijabi madaidaici, sannan kuma riƙe da wata kyakkyawar jaka a hannunta, kamar yadda hotunan na ta suka nuna.

Kara karanta wannan

"Abin Da Ciwo": Wata Da Ke Saudiyya Ta Yi Kuka Ganin Halin Da Yayanta Ke Ciki Duk Da Tana Turo Kudi Duk Wata

Nancy Isime ta kashe intanet da zazzafan hotunanta
Shigar jaruma Nancy Isime ta jawo zazzafar muhawara a kafar sada zumunta. Hoto: @nancyisimeofficial
Asali: Instagram

Ta bayyana a tare da hotunan, saƙon cewa ta samu damar ziyartar birnin Kano kan wani aiki na musamman da ya kai ta can. A cewarta:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yau dai na ziyarci kamfanin @vivaplusdetergent/@aspiranig da ke Kano, kuma na yi matukar farin ciki! #ProudVivaDiva. Bayanin ziyarar tawa na nan zuwa daga baya! Yanzu dai ya ya ku ka ga shigar tawa wacce @medlincouturecollection suka ɗinka mun domin ziyarar?”

Mabiyanta sun yi martani kan hotunan na ta

Masoyanta da ma wasu mashahuran mutane sun yi martani kan sabbin hotunan da Nancy ta ɗora a shafinta na Instagram.

Wasu daga cikin mabiyanta na ganin ta yi daidai, inda har suka ma yaba da kwalliyar ta ta, a yayin da wasu kuma suke ganin ba ta yi daidai ba na kwaikwayon al'adar waɗansu. Ga dai ra'ayoyin mabiyan na ta kamar haka:

Kara karanta wannan

"Ko Ni Kadai Ce Mai Irin Wannan Tunanin?" Kyakkyawar Bafulatana Ta Bayyana Irin Mijin Da Ta Ke Son Aure, Ta Bar Mutane Baki Bude

officialjet11 ya ce:

"Shin yanzu kin koma musulma ne, musulmi ba zai taɓa sanya sutura irinta kirista ba ko da zuwa ya yi gidan ki, ki mutunta kanki, ki daina siyar da ƙimarki."

ramsey_ng ya ce:

“Wannan ne dalilin da ya sa Arewa ta cancanci ta samu shugaban ƙasanta na daban, ta hakan ne mutane za su bi dokokin sanya irin tufafin da suka dace da al’adarsu da addininsu maimakon cusawa sauran al'umma al'amuran da su kawai ya shafa, saboda abinda suka yi imani da shi kenan."

delaniyai cewa ya yi:

"Wow Zai yi kyau sosai idan kika musulunta❤️ @nancyisimeofficial kin yi kyau sosai a cikin wannan hijabin."

nursem.o ya ce:

"Kyakkyawa MashaAllah."

jemimaosunde cewa ta yi:

"Sarauniyar kano gaskia ❤️❤️❤️ suna sonki!!!! sosai! mu ma muna son ki."

Jaruma Fati Muhammad ta kai ƙarar wani boka kotu bisa zargin damfara

Wani labarin da Legit.ng ta kawo muku a kwanakin baya, kun ji yadda Fati Muhammad, jarumar fina-finan Hausa wato Kannywood, ta kai ƙarar wani boka gaban kotun shari'ar Muslunci a Kano.

Kara karanta wannan

Shugabancin Majalisa: Cikakkun Bayanai Kan Ziyarar Yari Wajen Buhari a Daura Sun Bayyana

Jarumar dai ta zargi mutumin da sace ma ta mota a yayin da ta je wajensa neman taimako bisa sammu da take tunanin an yi ma ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel