Kyakkyawar Bafulatana Ta Bayyana Aniyarta Ta Yin Wuff Da Inyamuri, Bidiyonta Ya Yadu

Kyakkyawar Bafulatana Ta Bayyana Aniyarta Ta Yin Wuff Da Inyamuri, Bidiyonta Ya Yadu

  • Wata kyakkyawar budurwa musulma tsatson Fulani ta ɗauki hankula a yanar gizo sosai bisa irin mijin da ta ke son aura
  • Kyakkyawar budurwar ta bayyana burinta na auren Inyamuri a rayuwarta, inda ta ke mamakin ko ita kaɗai ce ke jin irin hakan
  • Mutane da dama tsatson Inyamurai sun yi mamakin hakan inda wasu da dama suka yi ta ƙarfafa mata guiwa

Wata kyakkyawar budurwa ƴar Najeriya wacce tsatson Fulani ce ta ɗauki hankula sosai a soshiyal midiya bayan ta bayyana cewa tana matuƙar son maza Inyamurai.

Kyakkyawar budurwar wacce Musulma ce sannan ƴar asalin jihar Kano, ta bayyana cewa tana fatan ta auri miji Inyamuri.

Kyakkyawar Bafulatana ta bayyana aniyar ta na yin wuff da Inyamuri
Bafulatanar tace tana fatan ta auri Inyamuri Hoto: @itzjiddaharnan
Asali: TikTok

Ta yi tunanin cewa ko ita kaɗai ce Musulma bafulatana mai irin wannan burin. Bidiyonta ya yaɗu sosai a TikTok, inda Inyamurai da dama suka riƙa nuna goyon bayansu a gareta.

Ƴan soshiyal midiya sun yi tsokaci

Wasu daga cikinsu sun yi amfani da wannan damar wajen nuna mata aniyarsu ta yin wuff da ita, yayin da suka yaba da kyawunta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga kaɗan daga ciki:

@jayblaq_ ya rubuta:

"Za ki samu wani nan ba da daɗewa ba sannan ƴaƴanki za su yi alfahari da ke kin samar musu mahaifi Inyamuri."

shred ya rubuta:

"A yanayin yadda kyawunki ya ke, Inyamuri ne kawai zai iya kula da ke, ki taimaka ki zo."

Diamond Goddess ya rubuta:

"Kada ki damu, nima Inyamuri ne zan haɗa ki da ɗan'uwa na.

theophelousmanfre ya rubuta:

"Barka da shigowa duniyar mu. Kina da kyau sosai."

MebbyRikky333 ta rubuta:

"Ba ke kaɗai ba ce nima ina irin wannan tunanin. Ina ta neman Inyamurin da za mu yi soyayya."

Musulma Yar Igbo Ta Magantu, Ta Ce Tana Matukar Alfahari

A wani labarin na daban kuma, wata musulma ƴar ƙabilar Igbo watau Inyamurai, ta yi bayani kan asalinta. Budurwar ta bayyana cewa ita musulma ce kuma iyayenta ma haka.

Matashiyar budurwar ta bayyana cewa tana alfahari da kasancewarta musulma kuma ƴar ƙabilar Igbo. Budurwar tace ta sha wuya wajen yin bayanin kalar addininta da ƙabilarta ga mutane saboda ba kasafai ake samun hakan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel