"Abin Da Ciwo": Wata Da Ke Saudiyya Ta Yi Kuka Ganin Halin Da Yayanta Ke Ciki Duk Da Tana Turo Kudi Duk Wata

"Abin Da Ciwo": Wata Da Ke Saudiyya Ta Yi Kuka Ganin Halin Da Yayanta Ke Ciki Duk Da Tana Turo Kudi Duk Wata

  • An wallafa wani faifan bidiyo inda wata mata da ke kasar Saudiya ta koka kan yadda ta ga ya'yarta ta dawo bayan barinta a gida
  • Matar mai suna Rina ta ce kullum karshen wata ta na turo makudan kudade don kula da 'yar amma ta ji takaicin ganinsa haka
  • Yayin da take maida martani ga mutanen da suka tofa albarkacin bakinsu, matar ta ce bata samu damar tafiya da yarinyar ba

Wata mata da take rayuwa a kasar ketare ta nuna bacin ranta a kafar sada zumunta ganin yadda 'yar cikinta ya dawo bayan barinta a gida.

Matar ta ce tana rayuwa a kasar Saudiya don ganin ta bai wa yaranta duk abin da suke bukata, amma ta yi mamakin yadda taga 'yar tata, cewar Legit.ng.

Kara karanta wannan

“Na Fada Maku Ni Mace Ce”: Budurwa Ta Saki Bidiyo Don Tabbatar Da Jinsinta, Mutane Sun Magantu

Mata ta fashe da kuka
Mata Ta Fashe da Kuka Ganin Yadda Danta Ya Kasance. Hoto: @rinaampire.
Asali: TikTok

Matar mai suna Rina ta ce ko wane wata ta na turo makudan kudade don kula da yarinyar , amma ba ta ji dadi ba bayan makwabtanta sun tura mata faifan bidiyon yaron.

Kalli faifan bidiyon a kasa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayin da take maida martanin mutane da dama da suka tofa albarkacin bakinsu, matar ta ce ba ta samu damar tafiya da yarinyar ba.

Martanin masu ta’ammalai da kafar sada zumunta ta zamani:

user6504831471730:

“Watakila kudin da ake turawa ana amfani da shi ne wurin siyan abinci, zai iya yiyuwa babban gida ne.”

user90309152136108betty holic:

“Allah ka kare mana yaranmu, ba wanda zai kula dasu kamar iyaye mata.”

rest:

“Ta na da lafiya sosai, wasu a kauye idan za su je majami’a suna saka sutura masu kyau,”

Wacera254:

“Abin takaici ne, amma idan ta na da lafiya duk mai sauki ne.”

Kara karanta wannan

“Bayan Shekaru 15 Da Aure”: Matar Aure Ta Koka a Bidiyo Yayin da Mijinta Ya Fada Mata Ita Ba Ajinsa Bace

Mama Roxie:

“Ina da labarin ‘yata da na bai wa wani dan uwana, a takaice kawai ‘nilimchkua’ wannan shi ne matakin da na dauka.”

Arianna wa alhajji 515:

“Kakata da tana ajiyemin kayana lokacin ina karami domin idan baki sun zo ko kuma lokacin biji in saka saboda ina yin datti da kayan.”

Bai Kyauta Ba: Dalibin Sakandare Ya Mari Kan Malaminsa, Uffan Bai Ce Ba, Bidiyon Ya Yadu

A wani labarin, an gano wano faifan bidiyo inda wani dalibi ya mari kan malaminsu yayin da yake musu bayani.

Mutane da dama sun soki dalibin da cewa ya nuna rashin da'a yayin da wasu kuma suke ganin abin nishadi ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel