An Gurfanar Da Wani Boka Gaban Kotu Bisa Zargin Sace Motar Jaruma Fati Muhammad

An Gurfanar Da Wani Boka Gaban Kotu Bisa Zargin Sace Motar Jaruma Fati Muhammad

  • Wani boka ya gurfana a gaban wata kotun shari'ar musulunci a Kano bisa zargin sacewa jaruma Fati Muhammad mota
  • Bokan ya haɗa baki ne da wani ɗan'uwanta inda suka ba ta wani rubutu ta sha wanda ya gusar mata da hankali
  • Kotun ta ɗage sauraron ƙarar bayan ta bayar da belin waɗanda ake zargi kan naira miliyan biyu da wasu sharuɗɗa

Jihar Kano - Wata babbar kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu a birnin Kano, ta tsare wani boka bisa zarginsa da laifin tafkawa fitacciyar jarumar masana'antar finafinan Kannywood, Fati Muhammad, sata.

Jaridar Aminiya ta kawo rahoto cewa ana zargin bokan ne da sace motar hawa ta jaruma Fati Muhammad.

An gurfanar da bokan da ya sace motar Fati Muhammad gaban kotu
Jaruma Fati Muhammad Hoto: @fatymuhd
Asali: Instagram

Tun da farko dai wani ɗan uwan jarumar ne, Sulaiman Kiyawa, ya zo gida ya same ta, ya gaya mata cewa an yi mata sammu amma zai haɗata da wani malami wanda zai ba ta taimako.

Ƴan sanda ne suka gurfanar da bokan bisa zargin ya sauya sunansa a wurinsu daga Isah zuwa Muhammad bayan ya haɗa baki da Kiyawa suka yi wa jaruma Fati Muhammad dadin baki cewar an yi mata sammu, suka ba ta wani rubutu ta kwankwaɗa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Takardar karar ta ci gaba da cewa bayan da jarumar ta sha rubutun ne hankalinta ya gushe, wanda hakan ya sanya suka yi amfaninda wannan damar suka yi maata awon gaba da mota.

Sun musanta zargin da ake mu su

Sai dai wadanda ake zargi sun musanta aikata laifin da ake tuhumar su da shi sannan suka nemi da kotun ta bayar da belin su.

Alkalin kotun mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya amince da bayar da belin su bisa sharaɗin sai wani mai riƙe da sarauta ya tsaya musu.

Mai riƙe da sarautar dole ya kasance dagaci ne ko mai unguwa wanda Sarki ne ya yi masa naɗin sarauta.

Sharaɗin kuma ya haɗa da sai an samu ma’aikacin gwamnati wanda ya kai matakin albashi na 15 wanda ya ke da gidan kansa a birnin tarayya Abuja.

Sannan sai an ajiye naira miliyan biyu (N2m) misalin rabin kuɗin motar da aka sacewa jarumar.

Alƙalin ya kuma sanya ranar 20, ga watan Yunin 2023, domin ci gaba da sauraron shari’ar.

Na So 'Ya'ya Na Su Yi Harkar Fim - Ali Nuhu

A wani labarin na daban kuma, jarumi Ali Nuhu ya bayyana cewa har a zuciyarsa ya so ƴaƴansa, su yi harkar fim amma sai suka nuna ba haka ba

Ali Nuhi ya bayyana cewa ƴaƴan na sa sun nuna ba su da ra'ayin bin sawunsa domin zama jarumai a masana'antar Kannywood.

Asali: Legit.ng

Online view pixel