Gwamnan Sakkwato Ya Gana da Shugabannin Tsaro Kan Harin da Yan Bindiga Suka Kai

Gwamnan Sakkwato Ya Gana da Shugabannin Tsaro Kan Harin da Yan Bindiga Suka Kai

  • Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato ya kira taron tsaro kan kazamin harin da yan bindiga suka kai ranar Asabar
  • Sabon gwamnan, wanda ya katse tafiyarsa zuwa Abuja, ya fara ɗaukar matakan kawo karshen 'yan bindiga a jihar
  • A ranar Asabar, wasu mahara suka yi ajalin mutane 37 a yankunan kananan hukumomin Tangaza da Gwadabawa

Sokoto - Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya kira taron majalisar tsaro na gaggawa ranar Litinin domin tattauna batun da ya shafi harin 'yan bindiga wanda ya ci rayukan mutane 37 ranar Asabar a arewacin jihar.

Jaridar Punch ta rahoto cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun kai kazamin hari kan mazaunan kauyuka uku a yankin ƙaramar hukumar Tangaza da wasu kauyuka biyu a yankin Gwadabawa.

Ahmed Aliyu.
Gwamnan Sakkwato Ya Gana da Shugabannin Tsaro Kan Harin da Yan Bindiga Suka Kai Hoto: Biyora Online TV
Asali: Facebook

Ƙauyukan da mummunan harin ya shafa sun haɗa da Raka, Raka Dutse da kuma Filin Gawa, inda maharan suka kashe rayuka 37, wasu da yawa suka ji raunuka.

Kara karanta wannan

Kashe-Kashen Zamfara: Sabon Gwamna Dauda Lawal Ya Daukarwa Zamfarawa Muhimmin Alkawari

Wane matakai gwamnan ya ɗauka don kare afkuwar haka nan gaba?

Gwamna Aliyu, wanda ya katse tafiyar da ya yi zuwa Abuja kan harin, ya lashi takobin hana 'yan bindiga da sauran yan ta'adda sakat a Sakkwato.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi ga yan jarida bayan kammala taro da shugabannin hukumomin tsaro da yammacin Litinin, Kakakin mai girma gwamna, Abubakar Bawa, ya faɗi wasu daga cikin abinda aka tattauna.

Ya ce daga cikin batutuwan da taron ya tattauna a kai shi ne lalubo yadda za'a gina dangantaka da jituwa a tsakanin hukumomin tsaro a jihar.

"Domin ta haka ne kaɗai za'a samu danganta mai kwari tsakanin jami'an tsaro da kuma ƴan banga a kokarin kawo karshen 'yan bindiga," inji shi.

Gwamnan ya kuma koka kan ayyukan Imfoma waɗanda a ganinsa ya kamata a tashi tsaye don kawo ƙarshensu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An Shirya Tsaf, 'Yan Kwadago Sun Janye Yajin-Aiki Bayan An Yi Kus-Kus a Aso Rock

Zamu biyan jami'an tsaro alawus ɗin da suke bi bashi - Gwamna

Bugu da ƙari, gwamnan ya yi alƙawarin biyan bashin alawus ɗin watanni 5 wanda dakarun rundunar sojin Operstion Hadarin Daji suka biyo gwamnatin jihar.

Haka zalika ya ce gwamnatinsa zata yi kokarin magance sauran kalubalen da rundunar take fuskanta domin ta ci gaba da aikin yaƙar yan ta'adda.

Daga karshe, ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu kan ya yi Addu'ar Allah ya saka musu da mafificin sakamako watau Aljanna.

Yan bindiga sun ƙara shiga Abuja

A wani rahoton na daban kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da Basarake da dasu mutum 2 a Abuja.

Bayanai daga mazauna garin da harin ya faru sun nuna cewa yan bindigan sun shafe sama da sa'a ɗaya suna cin karensu ba babbaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262