Budurwa Ta Fashe Da Kuka A Shago Bayan Shafe Makwanni 3 Babu Cinikin Ko Kwandala, Bidiyon Ya Bazu

Budurwa Ta Fashe Da Kuka A Shago Bayan Shafe Makwanni 3 Babu Cinikin Ko Kwandala, Bidiyon Ya Bazu

  • Wata budurwa ta fashe da kuka a wani faifan bidiyon TikTok bayan ta shafe makwanni 3 babu ciniki a shagonta
  • An gano budurwar tana zagayawa a shagon tana hawaye yayin da ta ke daukan faifan bidiyon da ya dauki hankulan mutane
  • Ta ce duk da irin rage farashin kayanta da ta yi amma babu wanda yazo ya siya kayan shagonta cikin makwanni 3

Wata budurwa 'yar Najeriya da take siyar da kayan kawa ta fashe da kuka yayin da ta duba taga bata ciniki a shagonta.

A wani faifan bidiyon TikTok, budurwar mai suna @cardi_b_trenche, an gano ta tana zagaya a cikin shagon tana hawaye.

Budurwa/shago/kuka/ciki/yar Najeriya
Budurwa ta ce babu mai siyan kaya a hannunta, Hoto: @cardi_b_trenche
Asali: TikTok

Ta ce bata yi ciniki ko sau daya ba a cikin makwanni uku duk da cewa ta karya farashin kayanta zuwa mai sauki.

Kara karanta wannan

Na Gaji: Mahaifiya Ta Ɗaure Ƙafar Ɗanta a Kujera Saboda Ɓarnar Da Yake Yi Mata a Shago

Sai dai ba ta yi karin haske kan farashin kayan nata na baya ba, amma farashin kayan nata na yanzu ya taba zukatan mutane.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Zaku iya kallon faifan bidiyon a kasa:

Jama’a da dama sun tofa albarkacin bakinsu ta kafar sada zumunta

Giftt Duff:

“Kiyi hakuri yarinya, kin yi binciki kuwa kafin ki bude wannan kasuwancin, saboda nima haka ta faru da ni.”

user7042703112175:

“Bai kamata kiyi kuka ba kanwata, tallata hajarki za ki yi har mutane su siya na tabbata za a samu sanji.”

IREGULA:

“Wurin kasuwanci yana da amfani sosai, ki duba wurin da kike kasuwancin abin da suke bukata ne, shin sun dace.”

DAMIEOHLAH:

“Wannan ya zama ruwan dare, nida kullum na ke yadawa ma babu wanda ya siya, amma nasan masu siya za su neme ni.”

Kara karanta wannan

Ni Kaɗai Za Ku Haifa: Yarinya Ta Shiga Ruɗani Bayan Ganin Mahaifiyarta Da Ciki

Niffy vic:

“Ki karanta Isaiah 60, Psalm 27 ki tofa a gishiri da ruwa a shagonki ki jira ikon Allah.”

Za ku iya kallon faifan bidiyo a kasa:

Na Tuba na bi Yesu: Budurwar Da Ke Tallan Hotunan Batsa Ta Mika Kanta Ga Yesu

A wani labarin, wata budurwa da take tallatawa da yada hotunanta a kafar sada zumunta ta ce yanzu fa komai ya sanja ta mika rayuwarta wa Yesu Kiristi, kuma haka zata kasance har karshen rayuwarta.

Ta yi nadaman yadda da take yada hotunan batsa da ke nuna sassan jikinta dan daukan hankalin maza, ta ce yanzu ta rungumi annabi Isa kuma ba dawowa baya zata rike addinita da gaskiya kamar sauran mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel