"Kadaici Ya Addabe Ni": Dirarriyar Matashiya Ta Koka a Yanar Gizo, Tana Neman Saurayi Ruwa Ajallo

"Kadaici Ya Addabe Ni": Dirarriyar Matashiya Ta Koka a Yanar Gizo, Tana Neman Saurayi Ruwa Ajallo

  • Wata matashiya ta bayyana cewa tana neman wanda za su yi soyayya saboda kaɗaicin da ya yi mata yawa bayan ta zama bazawara
  • Ta bayyana cewa shekarunta 32 sannan a shirye ta ke ta yi soyayya da matasan da shekarunsu sun kai 40 ko fiye da haka
  • Ta tura wani saƙo ne a sirrance zuwa ga @oku_yungx, wanda ya sanya shi a Twitter, inda ake ta sharhi sosai a kansa

Wata matashiya ta koka inda ta bayyana cewa tana neman wanda zai yi soyayya da ita saboda kaɗaici ya yi mata yawa.

Matashiyar wacce shekarunta 32 a duniya ta tura saƙon sirri ne zuwa ga @oku_yungx a Twitter, inda ta ke cewa tana son samun mashinshini a rayuwarta.

Matashiya na neman saurayi ruwa ajallo
Tace tana son mai shekara 40 ko fiye da haka Hoto: Getty Images/Srdjanns74. An yi amfani da hoton ne kawai
Asali: Getty Images

Ta bayyana cewa ita bazawara ce kuma bata da ɗa, wanda hakan ya sanya kaɗaici ya addabe ta sannan ta ke cikin matuƙar buƙatar samun masoyi.

Kara karanta wannan

“Na Gaza Numfashi”: Budurwa Ta Caccaki Fasinja Da Ya Dunga Tusa Duk Bayan Minti 15 a Jirgin Sama Daga Lagas Zuwa Casablanca

Tana son samun wanda ya ke da wadata sosai

Matashiyar ta bayyana cewa a shirye ta ke ta yi soyayya da matasan da sun kai shekara 40 ko fiye da hakan. Ta bayyana cewa dole ya zama akwai ƴan canji a hannunsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamanta:

"Barka da yamma. Shekaru na 32 kuma bani da yara. Kaɗaici ya addabe ni, ko zaka iya taimaka min ka wallafa saboda maza waɗanda suka ɗan kwana biyu (shekara 40), wanda ya ke son yin soyayya sannan yana da wadata sosai. Ina da aikin yi kuma. Nagode."

Saƙon na ta ya janyo cece-kuce a Twitter bayan an wallafa shi. Ga kaɗan daga ciki:

@roqzee said:

"Wanda ya ke da wadata" A wannan halin da Tinubu ya jefa mu? Omo tana buƙatar ta gyara abubuwan da ta ke nema, ko maza ƴan shekara 40 yanzu neman waɗanda za a raba ɗawainiya su ke. Kuma yakamata mu san cewa ko ta rabu da tsohon mijinta ne saboda tana yi mai duka.... abinda namiji zai iya yi mace ma za ta iya yin wanda ya fi shi."

Kara karanta wannan

"Hada Turo IV": Matashi Ya Koka Bayan Budurwarsa Za Ta Auri Wani Daban, Hirar Su Ta Bayyana

@AimThaMachine_ ya rubuta:

"Bazawara ƴar shekara 32 wacce ba ta da yara tana neman mai wadata ɗan shekara 40 a cikin wannan tattalin arziƙin da Buhari ya bar mu a ciki sannan yanzu Tinubu ya ɗora a kai, amma ba za a ji mutuwar sarki a baki na ba."

'Yar Shekara 123 Na Neman Mijin Aure

A wnai labarin na daban kuma, wata tsohuwa mai shekara 123 a duniya ta garzaya yanar gizo neman mijin aure.

Tsohuwar ta bayyana cewa ba ta taɓa sanin wanu namiji ba a rayuwarta kuma har yanzu sabuwa ce fil kamar budurwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel