"Hada Turo IV": Matashi Ya Koka Bayan Budurwarsa Za Ta Auri Wani Daban, Hirar Su Ta Bayyana

"Hada Turo IV": Matashi Ya Koka Bayan Budurwarsa Za Ta Auri Wani Daban, Hirar Su Ta Bayyana

  • Wani matashi ɗan Najeriya koka kan yadda budurwarsa ta shekara uku ta rabu da shi ta koma wajen wani saurayin
  • Matashin ya yi iƙirarin cewa har yanzu tana son shi, amma iyayenta ne suka tilasta mata cewa dole sai ta auri wani daban
  • Hirar da suka yi a WhatsApp ta nuna cewa har yanzu yana jin jiki dangane da cin amanar da budirwarsa ta yi masa

Wani matashi mai amfani da sunan @sadeeq_malo a Twitter, ya bayyana labarin yadda ya samu tangarɗa a soyayyarsa.

Matashin ya bayyana cewa da shi da budurwarsa sun kwashe shekara uku suna soyayya, sannan sun shirya yin aure.

Matashi ya koka bayan budurwarsa ta rabu da shi
Tace masa iyayenta ne suka tilasta mata Hoto: @sadeeq_malo
Asali: Twitter

Sai dai, abubuwa sun kwaɓe musu lokacin da iyayen budurwar ta sa suka shirya haɗa ta aure da wani daban.

Abubuwa sun sauya ba zato ba tsammani

Kara karanta wannan

Sabon Mulki: Kananan ’Yan Kasuwa Sun More, Abba Gida-Gida Ya Yafe Musu Biyan Haraji

A cewar matashin budurwar ta sa ta gaya masa cewa ba ta da wani zaɓi wanda ya wuce ta bi abinda iyayenta suke so.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa har yanzu tana son shi amma ba za ta iya bijirewa iyayenta ba. Ta roƙe shi da ya yafe mata ya ɗauka komai ba komai ba ne kawai ya ci gaba da rayuwarsa.

Matashin ya bayyana cewa lamarin ya girgiza shi matuƙa sannan bai yi tunanin za ta rabu da shi ba, bayan duk kasancewa taren da suka yi a baya.

Hirar da tsaffin masoyan suka yi ta nuna yadda matashin ya bayyana kaɗuwarsa da kuma halin baƙin cikin da ya tsince kansa a ciki.

A kalamansa:

"Budurwata za ta auri wani daban saboda matsin lambar iyaye. Shekarar mu uku muna tare. Ba kowace soyayya ba ce za ta kai ga aure. Ina miki fatan alkhairi."

Kara karanta wannan

Neman Suna: Matashi Ya Ciyo Bashin N500k Daga Banki, Ya Ba Budurwarsa Ta Sha Shagalinta

Labarin ya sanya mutane sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi a soshiyal midiya. Wasu sun tausaya masa inda suka shawarce shi da ya ɗauki ƙaddara ya manta da komai.

Matashi Ya Ciyo Bashin Banki Domin Ya Faranta Ran Budurwarsa

A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya yi ƙoƙarin faranta ran budurwarsa wacce ya ke matuƙar so a zuciya.

Matashin ya garzaya ya ciyo bashi inda ya ɗamka mata kuɗaɗen ta sha shagalinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel