“Mutumin Na Ta Sako Shi Duk Minti 10”: Budurwa Ta Ce Fasinja Na Ta Tusa a Jirgin Sama

“Mutumin Na Ta Sako Shi Duk Minti 10”: Budurwa Ta Ce Fasinja Na Ta Tusa a Jirgin Sama

  • Wata matashiyar budurwa da ta hau jirgin sama daga Lagas zuwa Casablanca ta bayyana mummunan halin da ta riski kanta
  • Matashiyar mai suna @iamrenike a Twitter ta ce akwai wani fasinja da ke ta tusa da gurbata iskar da mutane ke shaka
  • Ta ce ta gaza yin numfashi da kyau kuma cewa mutumin da ke ta tusa mugu ne

Wata matashiyar budurwa wacce ta shiga jirgin sama daga Lagas zuwa Casablanca ta ce akwai wani mutum da ke gurbata iskar da suke shaka.

Matashiyar mai suna @iamrenike a Twitter ta koka cewa fasinjan da take magana a kai yana ta tusa akai-akai.

Matashiya, wallafa da jirgi
Matashiya ta koka kan tusa da fasinja ya dungi yi a jirgin sama Hoto: Twitter/@iamrenike and Getty Images/Aaron Fosterm
Asali: UGC

Ta ce fasinjan na ta sakin tusa mai tsananin wari duk bayan minti 15, kuma cewa hakan ya jefa ta a cikin wani yanayi mara dadi ko kadan.

Kara karanta wannan

Tun Yanzu Wasu Kungiyoyi 3 Sun Fito Za Su Yaki Bola Tinubu Kan Cire Tallafin Fetur

Yanzu ta je Twitter don caccakar wannan fasinjan, amma bata ambaci sunan mutumin ba tunda bata sani ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta rubuta:

"Wannan ya tuna mani. Idan kaine mutumin da ke tusa duk bayan minti 10-15 a jere a jirgin Royal Air Maroc (Lagas zuwa Casablanca) a ranar 21 ga watan Mayu daga 7:10am zuwa 11:30am, ina so ka sani cewa mugu ne kai.
"Na fara magana da daga murya sosai a jirgi mai tafiyar awanni 4. Ka ji sosai kuma a bayyane ina gamawa sai ka saki wani."

Kalli wallafarta a kasa:

Jama'a sun yi martani

@ani_berny ta ce:

"Aikin mgunta tsantsa. Akwai wani mutum da nake hari wanda ke yawan nuna wannan muguntar a motar brt, na bi tusar har mazauninsa, abun bakin ciki shine tusar tasa na makalewa a jikin kayan wani kowa sai ya shiga rudani kan ainahin wanda ya yi tusar."

Kara karanta wannan

“Na Iya Girki Da Goge-Goge”: Budurwa Ta Fada Ma Hadaddan Gaye Yayin da Ta Yi Masa Tayin Soyayya a Bidiyo

@rotilaw ta ce:

"Kada ki zamo mai tsauri kan mutumin, ba ki san abun da shi ko ita yake fuskanta ba. Tusa, kamar yadda kika bayyana, suna faruwa ne sakamakon gajiya da ko kuma wani damuwa ko hadin abinci na gambiza."

Bidiyon Buhari ya bayyana a gidansa na Daura, an gano shi yana mike kafa

A wani labari na daban, wani bidiyo ya bayyana a soshiyal midiya inda aka gano tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yana mike kafa a gidansa na Daura.

A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu ne Buhari ya koma mahaifarsa da ke Daura bayan mika mulki ga shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel