"Ban Taba Sanin Wani Da Namiji Ba": Tsohuwa 'Yar Shekara 123 Na Neman Mijin Aure, Bidiyonta Ya Yadu

"Ban Taba Sanin Wani Da Namiji Ba": Tsohuwa 'Yar Shekara 123 Na Neman Mijin Aure, Bidiyonta Ya Yadu

  • Theresa Nyirakajumba ta koka a yanar gizo bisa rashin samun tsayayyen namiji wanda zuciyarta ke so da gaskiya
  • Tsohuwar ta koka kan cewa bata taɓa soyayya da wani namiji ba a rayuwarta, amma yanzu tana son samun wanda zai so ta
  • A cikin wani bidiyo mai sosa zuciya da tashar Afrimax English ta sanya, ta roƙi mutane da su taimaka mata samo wanda zai yarda su yi soyayya

Wata tsohuwar mata, Theresa Nyirakajumba, ta miƙa ƙoƙon barar ta ga ƴan soshiyal midiya da su taimaka mata wajen samo abokin rayuwa.

A wani bidiyo da aka sanya a Youtube, tsohuwar matar ta bayyana cewa bata taɓa yin soyayya da wani ɗa namiji ba, tun da ta zo duniyar nan.

Tsohuwa 'yar shekara 123 na neman abokin rayuwa
Tsohuwa 'yar shekara a duniya na neman mijin aure Hoto: Afrimax English
Asali: Youtube

Da ta ke tattaunawa da Afrimax English, ta bayyana yadda ta ƙi amsa tayin masu son ta da dama saboda tana jiran zuwan tsayayyen namiji wanda zuciyarta za ta yi maraba da shi.

Kara karanta wannan

Za A Sha Jar Miya: Yan Najeriya Da Kansu Za Su Roƙi Tinubu Ya Yi Tazarce, Betta Edu

Abin takaici hakan bai faru ba, sannan a yanzu da ta ke da shekara 123 a duniya, tana neman a taimaka mata wajen samo mata abokin rayuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zuciyarta bata taɓa son wani ɗa namiji ba

Ta bayyana a cikin bidiyon cewa:

"Ban taɓa yin aure ba a rayuwata. Eh tabbas babu namijin da ya taɓa sani na a ƴa mace. Lokacin ina budurwa na yi tunanin na ɗanɗana amma ba zan iya zuwa gidan mijina a hakan ba."
"Sunana Theresa Nyirakajumba. Ɓan taɓa ganin namiji a tuɓe ba. A tsawon shekara 123 na rayu da wani burin da bai cika ba na fatan cewa wata rana wani namiji zai fito wanda zuciyata za ta yi maraba da shi."
"A halin yanzu, za ku iya taimaka min ku kawo min abokin rayuwa. Lokacin da na ke budurwa bana son tarayya da maza, hakan ya hana ni yin soyayya. Ɓan taɓa son wani ɗa namiji ba."

Kara karanta wannan

"Bana Son Wayar N120k": Budurwa Ta Ki karbar Wayar Da Saurayinta Mai Samun N400k a Wata Ya Siyo Mata, Tace Sai Ta N345k

Albashinsa N400k": Budurwa Ta Hakikance Sai Saurayinta Ya Siyo Mata Wayar N345k

A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta taso saurayinta a gaba kan sai ya siyo mata tanfatsetsiyar wayar da kuɗinta sun kai N345k.

Saurayin na ta mai samun N400k a wata ya siyo.mata wayar N120k, inda tace bata son wannan sai dai babbar ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel