Gwamnatin Buhari Za ta Karrama Mashahurin Malamin Musulunci, Sani Rijiyar Lemu

Gwamnatin Buhari Za ta Karrama Mashahurin Malamin Musulunci, Sani Rijiyar Lemu

  • Gwamnatin tarayya za ta karrama Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu da lambar girma
  • Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu zai samu lambar OON saboda irin gudumuwar da yake badawa
  • Dr. Rijiyar Lemu wanda ya yi karatu a Saudi yana cikin manyan malaman addini masu karantarwa

Abuja - Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu yana cikin muhimman mutanen da gwamnatin tarayya za ta ba lambar karramawa na shekarar 2022.

Legit.ng Hausa ta fahimci gwamnatin Muhammadu Buhari za ta bada lambar girman OON ga babban malami, Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu.

A wata takarda da ta fito daga ofishin Ministan harkoki na musamman, an ji cewa an gayyaci shehin a cikin mutanen da za a karrama a shekarar bana.

Kamar yadda takardar da Mai girma Minista watau Sanata George Akume ya aikawa malamin ta nuna, za ayi wannan biki yau a dakin taro na ICC a Abuja.

Kara karanta wannan

Rikici: An farmaki hadimin Ganduje a Kano, ya ce 'yan Kwankwasiyya ne suka sace wayarsa

Ana sa rai yanzu haka Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu yana garin Abuja inda za ayi bikin.

Sani Rijiyar Lemu
Sheikh Sani Rijiyar Lemu OON
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wanene Sani Umar Rijiyar Lemu?

An haifi malamin musuluncin nan ne shekaru 52 da suka wuce a garin Makka a kasar Saudi Arabiya, sai daga baya ya dawo asalin kasarsa ta Najeriya.

Bayan ya fara karatu a gida, daga baya malamin ya koma jami’ar Madinah inda ya yi digirin farko zuwa na uku duk a bangaren hadisin Manzon Allah (SAW).

Shehin ya rubuta littatafai da-dama a Najeriya da kasar waje. Daga ciki akwai Nabiyyur Rahma na tarihin Annabi (SAW) da Tafsrin Kur’ani da Hausa.

Yanzu haka mataimakin Farfesa ne a jami’ar Bayero da ke Kano, kuma Darekta a sashen addinai. Rijiyar Lemu yana kuma koyawar a jami’ar Al Qalam.

Sheikh Rijiyar Lemu yana darasin Tafsir a Kano da Bauchi a lokacin azumi da kuma karatun wasu littatafan musulunci da sun zagaya kasashe na Duniya.

Kara karanta wannan

Kano: Gini Mai Hawa Ɗaya Ya Rufta Wa Yara 3 Yan Gida Daya, Biyu Cikinsu Sun Mutu

Sauran wadanda za a ba lambar OON sun hada da Dr. Bashir Aliyu Umar da Tajudden Adigun.

Ana ta 'yan maganganu

A makon da ya gabata, kun ji rahoto cewa akwai masu korafi saboda sun fahimci irin mutanen da gwamnatin Muhammadu Buhari za ta ba lambar girma.

Kungiyoyi masu zaman kansu sun koka da cewa ‘yan siyasa suka ciki jerin sunayen da aka gani, alhali akwai sauran ‘Yan Najeriya da suka dace da lambar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel