Buba Galadima: Mutum 440 Cikin Wadanda Buhari Ya Ba Wa Lambar Yabo Ya Kamata Suna Gidan Yari

Buba Galadima: Mutum 440 Cikin Wadanda Buhari Ya Ba Wa Lambar Yabo Ya Kamata Suna Gidan Yari

  • Buba Galadima, tsohon na hannun daman Shugaba Muhammadu Buhari ya soki lambar yabo na kasa da Buhari ya ba mutane 470 a baya-bayan nan
  • Galadima ya ce galibin wadanda aka ba wa lambar yabon kamata ya yi suna gidan yari inda ya kira lamarin 'lambar yabo na yara'
  • Jigon na NNPP ya ce a ganinsa mutane da suka yi wa kasa aiki suka yi ritaya ba tare da EFCC ko ICPC na binsu ba ne ya dace a rika bawa lambar yabon

Tsohon na hannun daman shugaban kasa Muhammadu Buhari, Buba Galadima ya soki lambar yabo ta kasa da shugaban kasa ya bawa wasu mutane a baya-bayan nan, rahoton The Punch.

Ya yi ikirarin cewa mutane 440 cikin 470 da aka karrama ya kamata suna gidajen yari a sassan kasar a hiran da aka yi shi a Arise TV a ranar Juma'a 14 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida: Ba Za Mu Sake Yarda Da Wani Zabe Na 'Inconlusive' Ba A Kano

Buba Galadima
Buba Galadima: Mutum 440 Cikin Wadanda Buhari Ya Ba Wa Lambar Ya Kamata Suna Gidan Yari. Hoto: Nigerian Tribune.
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Idan ka ce Buba Galadima, ka yi amfani da Injiniya, Alhaji ko wani abu? Ban taba karbar sarauta ba kuma ko Galadima, idan da yadda na so kuma ba don yana takardun karatu na daga frimare zuwa jami'a ba, da na cire kalmar (Galadima) don sarauta ce kuma bana bukata.
"Bari in fada maka, cikin mutum 447 da aka bawa lambar yabo na kasa, ina tunanin 440 cikinsu kamata ya yi suna gidan yari a maimakon gabatar da su a matsayin wadanda suka cancani karramawa. Menen dalilin karramawar? Wace karamci suke da shi?
"Sakayya ne kawai ga yara kuma ka zan Muhammadu Buhari da kansa ya zargi Cif Olusegun Obasanjo, marigayi Musa Yar'Adua da Goodluck Jonathan ta bada lambar yabo, da karrama mutanen da akwai alamar tambaya a halayensu."

Kara karanta wannan

Zan Tabbatarwa 'Yan Najeriya Tsaro Kafin Na Mika Mulki, Buhari Ya jaddada

Ya cigaba da cewa:

"Wanene cikin wadanda aka bawa lambar yabon ke da halin kirki tas? a gani na, kamata ya yi a rika bada irin wannan lambar yabon ga mutanen da suka yi ritaya daga aiki kuma EFCC da ICPC ba su rika binsu ba.
"Kazalika, a rika bawa wadanda suka mutu yayin yi wa kasarsu hidima. Gara in bawa mai girki da ya iya dafa abinci maimakon mai sayar da katin waya da ya zama tiriloniya kuma wannan shine ra'ayi na."

Dan siyasan ya kuma ce yana kyautata zaton dan takarar shugaban kasa na jam'iyyarsa ta NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso zai yi nasara a zaben 2023, duba da irin ayyukan da ya yi matsayin ma'aikacin gwamnati.

Shugaba Buhari Ya Karrama Buratai Da Babban Lambar Yabo Na Kasa

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon babban hafsan sojojin kasan Najeriya kuma jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, T.Y. Buratai ya shiga jerin wadanda za su samu lambar yabo ta kasa na 'Commander of the Order of the Federal Republic', (CFR).

Kara karanta wannan

Rikici: Tashin hankali yayin da kanin miji ya kwace wa dan uwansa mata mai 'ya'ya 7

Tsohon shugaban sojojin da wasu fitattun yan Najeriya guda 436 ne za a karrama da lambar yabon a wannan shekarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel