Tashi Ka Nemi Abun Yi: Fusatattar Matar Aure Ta Dangwararwa Da Miji Kwano Babu Abinci

Tashi Ka Nemi Abun Yi: Fusatattar Matar Aure Ta Dangwararwa Da Miji Kwano Babu Abinci

  • Wata mata ta ja hankali sosai a TikTok bayan ta gabatarwa mijinta da kwano babu abinci a ciki a wani bidiyo da ya yadu
  • Ta dangwaran masa da rufaffen kwanon a kan teburin gabansa sannan ta bukaci da ya fita ya nemi aiki, tana mai cewa bai san komai ba sai ci
  • Masu amfani da TikTok da dama sun sanya baki cikin lamarin yayin da suka bayyana ra'ayoyinsu

Masu amfani da TikTok sun yi martani ga wani bidiyo na wata mata da ta gabatarwa mijinta kwano wayam babu abinci a ciki.

A cikin bidiyon, mutumin ya zauna yana jiran a kawo masa abincinsa, kawai sai gashi an dangwaran masa da kwano babu komai.

Mata da miji
Tashi Ka Nemi Abun Yi: Fusatattar Matar Aure Ta Dangwararwa Da Miji Kwano Babu Abinci Hoto: TikTok/@sibiaokemwa.
Asali: UGC

A cewar matar, mutumin bai da wani aiki sai na tambayar abinci ba tare da fita aiki ko kawo gudunmawar komai ba.

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Fashe Da Kuka Yayin da Aka Yi Mata Kwalkwabo Bayan Mutuwar Mijinta, Bidiyon Ya Taba Zukata

Ta bukaci mutumin da ya je ya nemi aiki don ya fara kawo nasa gudunmawar. Mutumin ya kadu da abun da matar tasa tayi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Koda dai bidiyon ya yi kama da zolaya, mijin ya ci fuska kuma hakan ya janyo martani. Ga wasu daga cikin martanin a kasa:

@user6042534519611 ya ce:

"Kara yaji dan Allah."

@tracyannandem ta yi martani:

"Malami ki ba mutumin cokali mai yatsu kuma ina nikakken timatir da yaji."

@rose_pro6 ta ce:

"Kwarai kwarai idan namiji baya aiki baya cin abinci."

@Candy ta yi martani:

"Bani da matsala da miji mara aiki ina dai da matsala da mijin da ke jin dadin rashin aikin."

@Vera Tull ta ce:

"Yayi maki kyau yarinya, yana da waya amma bai da aikin yi."

Matashiya Ta Fashe Da Kuka Yayin da Aka Yi Mata Kwalkwabo Bayan Mutuwar Mijinta, Bidiyon Ya Taba Zukata

Kara karanta wannan

Fasaha Tsantsa: Yadda Wani Dan Najeriya Ya Mayar Da Kwantena Ya Zama Hadadden Ofis, Bidiyon Ya Yadu

A wani labarin, wata matashiya yar Najeriya mai shekaru 23, ta yi alhinin rashin mijinta a shafin soshiyal midiya bayan ya yi mutuwar faran daya.

An gano matashiyar wacce ke juyayi a cikin wani bidiyon TikTok a yanayi na alhini da hawaye a idanunta yayin da wasu taron mata ke aske mata gashin kanta.

Ta koka cewa abun akwai ciwo sosai yadda ya zama bazawara a karancin shekaru irin nata. Ta tambayi dalilin da yasa mutumin bai tsaya ba bayan sun shirya yadda rayuwarsu Za ta kasance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel