"Daga Yar Aiki Ta Zama Matan Mai Gida": Budurwa Ta Girgije A Bidiyo Don Farin Ciki

"Daga Yar Aiki Ta Zama Matan Mai Gida": Budurwa Ta Girgije A Bidiyo Don Farin Ciki

  • Wata mata yar Najeriya ta bayyana farin cikinta a kafar sada zumunta bayan samun karin girma daga yar aiki zuwa matan gida
  • Yayin da ta ke nuna wa duniya juna biyu da ta dauka, matar cike da murna ta bayyana yadda ta fara a matsayin yar aiki a gidan masoyinta
  • Daga bisani, mai gidanta ya fara sonta kuma matsayinta ya canja daga yar aiki zuwa matar gida

Wata mata mai juna biyu ta bawa mutane labarin soyayyar ta mai ban mamaki.

A cewar matan mai suna simplisauce a TikTok, bayan ta kammala makarantar sakandare, zabi biyu da ta ke da shi sune zama yar aikin gida ko kuma bin mazaje.

Budurwa
"Daga Yar Aiki Ta Zama Matan Mai Gida": Budurwa Ta Girgije A Bidiyo Don Murnar. @simplisauce.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

A Raba Aurenmu Don Baya Aikin Komai Sai Jajibe-jajiben Fada, Matar Aure Ta Roki Kotu

Ta zabi ta zama yar aikin gida kuma bayan watanni kadan, soyayya ya shiga tsakaninta da mai gidan da ta ke aiki.

Daga bisani ta dauki juna biyu kuma ya daga darajarta zuwa 'matar gida'. Amma, ta ce bai riga ya aure ta ba tukuna.

Da ta ke wallafa bidiyon a Tiktok, ta ce:

"Daga yar aikin gida zuwa matar gida. Bayan kammala makarantar sakandare, zabi biyu suka rage min. Bin mazajen banza ko neman aiki nagari. Na zabi in fara aiki a matsayin mai shara a wannan gidan. Wata biyu da fara aiki, mai gida ya fara nuna ra'ayin so na. Ina ce dai abu ne irin na maza. Ashe Ubangiji ya ke son tallafa wa rayuwata."

A wani bidiyon daban, an hange ta kwance a gado yayin da masoyinta ke mata liki da kudi. Ta kambama kanta cewa duk safe da kudi ake tashinta daga barci.

Mutane sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi game da bidiyon:

Kara karanta wannan

Ruwan dare: Budurwa ta jawo cece-kuce yayin da ta kammala digiri, tace za ta rushe gidansu

@speciallove91 ta ce:

"Haka wata yar aikin za ta zo gidan."

@jojaxon ta rubuta:

"Hmmm kin tabbatar ainihin matar gidan ba ta kasar waje. Ku yi tunani sosai."

@jennyeventsandcakes ta ce:

"Ina taya ki murna ki bani aikin kawata wurin biki idan lokacin ya zo."

@maryemmanuel162 ta yi martani:

"Ina matar mai gidan? Ina fatan bai taba aure a baya ba?".

Bidiyon Budurwa Tana Sharbar Kuka Saboda Saurayin Da Suka Fara Soyayya Tun Karamar Sakandare Ya Rabu Da Ita

A wani rahoton, duk lokacin da mutane suka yi da ce da masu kaunarsu, ba su son wani abu da zai janyo matsala ko rabuwa tsakaninsu.

Amma dai wasu lokutan, wasu dalilai na janyo rabuwa tsakanin masoya ko da kuwa sun dade suna soyayyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel