Yadda Aka Fallasa Wani Mutum Da Ke Bara Da Yara Masu Ciwon Ciki Na Karya A Legas

Yadda Aka Fallasa Wani Mutum Da Ke Bara Da Yara Masu Ciwon Ciki Na Karya A Legas

  • An kama wani mutum, Onyedinka Esiala, da ke amfani da kananan yara masu ciwon ciki na karya yana bara a Legas
  • Asirinsa ya tonu ne yayin da wani da ke wucewa ya ganshi da yara sannan ya fallasa cewa lafiyarsu kalau
  • Esiala ya amsa cewa yaran lafiyarsu kalau, amma wani Uche, mai gidansa na kawo su daga kauye yana basu wani magani su sha sai cikinsu ya kumbura idan za su fito bara

Legas - An kama wani mutum mai matsakaicin shekaru, Onyedinka Esiala, dan asalin jihar Enugu. An kama shi a ranar Laraba yana amfani da yara masu ciwon ciki na karya don bara a unguwar Mile 2, Legas.

Wanda ake zargi
Yadda Aka Fallasa Wani Mutum Da Ke Bara Da Yara Masu Ciwon Ciki Na Karya A Legas. Hoto: @VanguardNGA.
Asali: Twitter

Yadda asirin Esiala ya tonu

Wani mutum da ke wucewa, mai suna Benefit ne ya tona wa Esiala asiri. Yayin magana da Vanguard, ya zargi wani Uche, mai gidansa, da koya masa damfarar.

Kara karanta wannan

Dawisun Namiji Mai Kyawawan Mata 8 Ya Ce Wasu Cikinsu Na Kishi Da Shi, Hotuna Sun Bayyana

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi ikirarin cewa Uche yana kawo yara Legas daga kudancin Najeriya a duk shekara idan ya tafi gida.

Wani bangare cikin abin da ya fada:

"Suna na Onyedinka, ni dan jihar Enugu ne. Mai gida na shine Uche. Da na taho daga kauye, ban samu aiki ba; mai gida na ya ce in taimaka masa in rika fito da yaran nan suna bara."

Iyayensu mata sun san abin suke yi a Legas

Ya cigaba da cewa:

"Duk lokacin da zan fito da su daga Orile zuwa gadan Mile 2, mai gida na zai basu wani kwayan magani da zai sa cikinsu ya kumbura na awanni, kuma yaran da iyayensu sun sani. Iyayensu mata na kauye.
"Yaran na zaune da su a kauye kafin su bawa mai gida na ya taho da su Legas. Yan matan ba yan uwa na bane, amma mahaifiyansu na kawo su wurin mai gida na. Wasu yaran suka yi shekara tare da mu, iyayensu mata ake bawa rabin kudin da suka samu wurin bara. Mai gida na yana basu wani bakin kwayan magani. Ban san sunan maganin ba. Bai fada min ba amma baki ne."

Kara karanta wannan

Fasaha Tsantsa: Yadda Wani Dan Najeriya Ya Mayar Da Kwantena Ya Zama Hadadden Ofis, Bidiyon Ya Yadu

Yara da ake bara da su
Yaran masu ciwon ciki na karya da ake bara da su a Legas. Hoto: @VanguardNGA
Asali: Twitter

Bayan gama masa tambayoyi, an tafi da Oyedinka ofishin yan sandan Najeriya da ke Area E, Festac aka mika shi hannun jami'an tsaron.

Bidiyon Yadda Aka Fallasa Wata Budurwa Da Ke Bara Da Jinjirin Karya A Lagas

A wani rahoton, yan Najeriya sun kadu bayan ganin wani bidiyo na wata matashiyar budurwa da ke amfani da jaririn bogi tana bara da rokon kudi a jihar Lagas.

A cikin bidiyon, matashiyar budurwar ta nannade wani abu a tsumman jego sannan tana lallashinsa kamar yaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel