Kishin Hauka: An Daure Mata a Gidan Yari Saboda Ta Kashe Jikanta da Ruwan Acid

Kishin Hauka: An Daure Mata a Gidan Yari Saboda Ta Kashe Jikanta da Ruwan Acid

  • An kai wata Hauwa Ibrahim kara a gaban kotun majistare a Garin Kano, ana zarginta da laifin kashe jariri
  • Abin mamakin shi ne wannan mata ta aika jikanta barzahu ne da hannunta domin ta taya surukarta yi kishi
  • Ganin ba su samu namiji ba, sai yaronta ya kara aure, da aka haifi namiji ne mahaifiyarsa ta kashe jinjirin

Kano - Wata mata mai suna Hauwa Ibrahim tana gidan gyaran hali a yanzu a dalilin kashe jikanta, wannan ya faru ne a jihar Kano.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Talata, 7 ga watan Satumba 2022 cewa Hauwa Ibrahim mai shekara 45 ta amsa laifinta.

Hauwa Ibrahim tana zama ne a unguwar Tugar Bala a karamar hukumar Bagwai da ke Kano, an kai ta kara a wani kotun majisare.

Kara karanta wannan

Budurwa Tayi wa Banki Fashi Don ta Samu Kudin Maganin Kansar 'Yar Uwarta

Ana shari’a da ita a kotu bisa zargin kashe wani jikanta da aka haifa, kuma ta amsa cewa lallai ta aikata wannan mummunan aiki.

Yadda abin ya faru - Lauya

Barista Ahmed Muhammad ya shaidawa kotu yadda wannan mata ta kashe jaririn da aka haifawa 'dan ta saboda mugun bakin kishi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lauyan yace yaron wannan mata bai samu namiji a Duniya ba, hakan ta sa ya yi wa matarsa kishiya, ya auro wata matar dabam.

Jariri
Wani jariri a kasar waje Hoto: www.freepik.com
Asali: UGC

Tun da yake tare da matarsa ba ta taba haihuwar namiji ba, amaryar mai suna Badariyya Ibrahim, tana zuwa tayi dace da 'da.

Ganin Badariyya Ibrahim ta haifi ‘da namiji wanda mai gidansu ya dade yana nema, sai tayi amfani da ruwan acid, ta kashe jaririn.

Rahoton yace Hauwa Ibrahim tayi wannan mugun aiki ne a lokacin da mai jego ta shiga ban-daki, ta aika jikanta zuwa barzahu.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya jawo cece-kuce yayin da ya fara birgima a kasa lokacin da matarsa ta haihu

Mai shari’a Haulatu Magaji Kankarofi ta saurari karar a ranar Talata, ta bukaci a cigaba da tsare wanda ake zargi a gidan yari.

Haulatu Magaji Kankarofi tace za a cigaba da sauraron shari’ar nan a ranar 4 ga watan Oktoba, wannan mata ta ragewa kotu aiki.

Lizz Truss ta zama PM

Kun samu labari cewa Mary Elizabeth Truss mai shekara 47 ta zama Shugabar Birtaniya, ita ce mace ta uku da ta dare kujerar nan.

Lizz Truss tayi aiki da Firayim Ministocin Ingila uku da suka shude kafinta. An zura ido domin ganin ta inda Truss za ta kamo kan mlki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel