Budurwa Tayi wa Banki Fashi Don ta Samu Kudin Maganin Kansar 'Yar Uwarta

Budurwa Tayi wa Banki Fashi Don ta Samu Kudin Maganin Kansar 'Yar Uwarta

  • Wata mata ta kai hari wani banki a Beirut da bindigar wasan yara inda ta kwashi kudi kusan dala 13,000 saboda 'yar uwarta
  • Ta yi hakan ne domin samun kudin siyan maganin cutar kansa dake damun 'yar uwarta wanda bankin ya rike
  • Ta wallafar bidiyon yadda tayi fashin a Facebook inda tace sun adana dala 20,000 kuma suna neman kudin magani dala 50,000

Wata mata ta yi fashi a bankin Beirut a ranar Laraba da bindigar yara kuma ta fita da dubban daloli domin biyan kudin maganin cutar dake damun 'yar uwarta sakamakon rikicin da ya bakunci Lebanon, Punch ta rahoto.

Wannan dai shi ne na baya-bayan nan a jerin gwano da aka yi a kasar Lebanon, inda aka hana kudaden ajiyar masu ajiya a bankuna kusan shekaru uku, lamarin da ya bar su cikin mawuyacin hali tare da tabarbarewar tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Elizabeth II: Za a Kashe Kusan Naira Biliyan 4 Wajen Bikin Jana’izar Sarauniyar Ingila

Lady Robs bank
Budurwa Tayi wa Banki Fashi Don ta Samu Kudin Maganin Kansar 'Yar Uwarta. Hoto daga lailanews.com
Asali: UGC

Sali Hafiz ta fitar da wani faifan bidiyo kai tsaye a Facebook na wani hari da ta kai a reshen bankin Blom na Beirut, inda aka ji ta tana kururuwa ga ma’aikatan banki da su saki wasu kudade yayin da aka rufe hanyoyin shiga bankin.

"Ni ce Sali Hafiz, na zo yau don in dauka ajiyar 'yar uwata da ke neman mutuwa a asibiti."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ban zo don in kashe kowa ba ko in tada gobara ba. Na zo ne domin neman hakkina.”

- Tace

Channels TV ta rahoto cewa, a wata hira da wata kafar yada labarai ta Lebanon bayan harin, Hafiz ta ce ta yi nasarar kwaso da kusan dala 13,000 daga cikin dala 20,000 da ta ce danginta sun ajiye.

Maganin ciwon daji na 'yar uwarta ya kai dala 50,000, in ji ta.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya jawo cece-kuce yayin da ya fara birgima a kasa lokacin da matarsa ta haihu

Wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP da ke wurin ya ce an zuba fetur a bankin a lokacinkuma gobara ta tashi wacce ta dauka kasa da sa’a guda.

Hafiz ta shaida wa kafafen yada labarai cewa ta yi amfani da bindigar wasan yara na 'ya'yanta wajen kai farmakin.

Wakilin AFP ya ce Hafiz da wadanda ake zargi da hannu a ciki sun tsere ne ta wata taga da ke bayan bankin kafin isowar jami’an tsaro.

Har yanzu dai ana nemanta kamar yadda 'yan uwanta suka bayyana, yayin da hukumar tsaron kasar ta Lebanon ta musanta jita-jitar cewa ta fice daga kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel