Abubuwa 10 da Za a Sani a Kan Matar da ta Zama Sabuwar Firayim Ministar Birtaniya

Abubuwa 10 da Za a Sani a Kan Matar da ta Zama Sabuwar Firayim Ministar Birtaniya

  • Watanni kusan biyu da Boris Johnson ya yi murabus, an zabi wanda za ta maye gurbinsa a kujerar Firayim Minista
  • Misis Liz Truss aka zaba ta karbi jagorancin Birtaniya, wannan ne karo na uku da mace za ta dare kujerar nan a Ingila
  • An haifi Truss a Oxford, za a iya cewa ta rika tsilla-tsilla a siyasa daga kuruciyar ta zuwa yanzu da tayi suna a Duniya

Elizabeth Truss tana da shekara 47 yanzu haka a Duniya, kuma ta haifi ‘ya ‘ya biyu, ta shiga siyasa bayan tayi aikin Akanta.

Legit.ng Hausa ta tattaro maku kadan daga cikin tarihin Liz Truss daga rahotannin Economic Times da kuma Times:

1. Da farko an san Liz Truss ne da sunan Elizabeth, an haife ta a garin Oxford, tayi karatun ilmin siyasa da tattalin arziki a jami’ar Merton College a 1996.

Kara karanta wannan

Tsohon Jigon Jam’iyya Ya Fadawa Peter Obi Sirri 5 Na Lashe Zaben Shugaban Kasa

2. Rahoton Times yace Truss ta taba bin mahafiyarta wajen yi wa Margaret Thatcher zanga-zanga. A jami’a, an san ta a matsayin ‘yar Liberal Democrats.

Daga baya Truss ne ta canza ra’ayin siyasa, ta shiga jam’iyyar Conservative Party a 1996. A yau ita ce take jagorantar wannan jam’iyya mai mulki a Birtaniya.

3. Truss ta auri Hugh O’Leary a shekarar 2000 wanda shi ma Akanta ne irinta, ma’aurantan sun haifi ‘ya ‘ya mata biyu, duk da an samu matsala, har yau suna tare.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

4. Sabuwar Firayim Ministar tayi aiki a kamfanin Shell tsakanin 1996 da 2000 a matsayin Akanta. Daga 2020 zuwa 2005, tayi aiki da by Cable & Wireless.

Liz Truss
Sabuwar Firayim Ministar Birtaniya, Liz Truss Hoto: AFP/Getty
Asali: Getty Images

5. Tun 2021 ta zama Ministar harkokin kasar waje da kasashen renon Birtaniya da cigaban kasa, a 2019 ta rike Ministar harokin mata da daidaito a Ingila.

Kara karanta wannan

Dalilan da suka Jawo Tinubu da Gwamnoni 5 Suka Ziyarci Jonathan Sun Farawa Fitowa

6. Truss ta zama ‘yar majalisa a shekarar 2010, tana wakiltar shiyyar Kudu maso yammacin Norfolk bayan an zarge ta da laifin lalata da wani ‘dan siyasa.

7. ‘Yar siyasar tayi aiki a karkashin Gwamnatocin David Cameron, Theresa May da kuma Boris Johnson, wadanda suka yi mulkin Birtaniya a jam’iyyarta.

8. Bayan David Cameron ya yi murabus, sai Truss ta zama Ministar shari’a, a tsawon tarihin wannan ofis na shekaru fiye da 1000, maza ke rike da shi.

9. Idan ta shiga ofis, Lis Truss za ta zama Firayim Minista ta 56 a tarihi. Kafin ita, mata biyu sun hau wannan kujera - Margaret Thatcher da Theresa May.

Abin da hakan yake nufi - Masani

Mun tuntubi Malam M. Bello (Malam MB) wanda masani ne a kan harkar gidan sarautar Birtaniya domin jin ra'ayinsa a game da nadin Misis Liss Truss.

Malam MB yace a lokacin Truss tana shekara 19, ta goyi bayan a rusa tsarin sarautar Ingila, wanda hakan babban sabo ne, ta taba goyon bayan hallata tabar wiwi.

Kara karanta wannan

Al’ada Mai Ban Sha’awa: Bidiyoyin Shagalin ‘Lugude’ Na Bikin Ruqayya Bayero, Amarya Da Kawayenta Sun Sha Daka

Masanin yace a makon jiya, Truss tana rike da Ministar harkokin kasashen waje, tayi wata katabora a kan shugaban Faransa, wanda hakan ya jawo surutu a Turai.

Uwa-uba, Malam MB ya nuna a baya 'yar siyasar ba ta goyon bayan Brexit. A cewarsa, abin tambayar ita ce, shin Firayim Ministar za ta farfado da tattalin Ingila?

Dokar Zaben Najeriya

Kun ji labari ‘Dan Majalisar Kogi, Smart Adeyemi yana so ayi kwaskwarima a dokar zabe da za ta haramta tikitin Kirista-Kirista ko Musulmi-Musulmi.

Amma abin mamaki, Sanata Smart Adeyemi wanda ya shigar da dokar yana goyon bayan Bola Tinubu da Kashim Shettima a 2023, duk da musulmai ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel