2023: Wani mutumin Kano ya fara tattaki daga Abuja zuwa Legas don goyon bayan Tinubu ya gaji Buhari

2023: Wani mutumin Kano ya fara tattaki daga Abuja zuwa Legas don goyon bayan Tinubu ya gaji Buhari

  • Wani mutumi ɗan asalin jihar Kano ya kuduri aniyar yin tattaki tun daga Abuja zuwa Legas domin nuna wa Tinubu ana tare
  • Hussein Lawan ya ce zai yi wannan sadaukarwa ne a madadin matasa ya roki Tinubu ya fito takara don tallafawa matasa
  • A cewarsa, Tinubu ne amsa mai kyau da zai karbi Najeriya ya gyara mata fasali domin matasa su fita daga kangin da suke ciki

Abuja - Mutumin mai suna Hussein Lawan, ɗan asalin garin Durun, ƙaramar hukumar Kabo a jihar Kano, ya fara tattaki ranar Laraba daga Abuja zuwa Legas.

Mutumin ya fara wannan doguwar tafiya ne domin nuna goyon bayan takarar jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Bola Tinubu
2023: Wani mutumin Kano ya fara tattaki daga Abuja zuwa Legas don goyon bayan Tinubu ya gaji Buhari Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Lawan ɗan kimanin shekara 30 a duniya ya zanta da manema labarai kafin ya tsunduma wannan tattaki daga Abuja City Gate.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Kotu zata fara zama kan bukatar FG na mika Abba Kyari kasar Amurka

Lawan na rike da wata karamar jaka da hoton Bola Tinubu, kuma ɗauke da rubutu, "Domin cigaba, Ahmed Bola Tinubu a 2023. Tabbatacciyar amsa kuma magajin Baba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Menene manufar Lawal na yin wannan tafiya a kafa?

Da yake jawabi ga manema labarai, Lawan ya ce:

"Ina son yin sadaukarwa ne ga matasan Najeriya ta hanyar yin tattaki da kafa daga Abuja zuwa Legas na roki Bola Tinubu ya nemi takara ya gaji shugaba Buhari."
"Idan kuɗine, ya na da su, muna bukatar ya zama shugaban ƙasa domin gyara Najeriya. Yana bukatar mulki domin canza fasalin matasa waɗan da suke shan baƙar wahala karkashin gwamnatocin baya."
"Saboda haka, daga nan City Gate Abuja, zan fara tattaki na zuwa Legas. kuma zan tsaya ne a filin Tafawa Balewa Square."

A wani labarin na daban kuma mataimakin gwamnan Kebbi ya sha da kyar yayin da yan bindiga suka buɗe wa tawagarsa wuta a wurin jaje

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsohon dan wasan kwallon Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce a Jos

Yan bindiga sun farmaki tawagar motocin mataimakin gwamnan jihar Kebbi yayin da yaje ta'aziyyar kashe mutane a Kanya.

Rahoto ya nuna cewa jami'an tsaron dake tare da shi sun yi batakashi da maharan, kuma ɗan sanda mai mukamin ASP ya rasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel