Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kai wa Mataimakin Gwamna hari a kan hanya

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kai wa Mataimakin Gwamna hari a kan hanya

  • Yan bindiga sun farmaki tawagar motocin mataimakin gwamnan jihar Kebbi yayin da yaje ta'aziyyar kashe mutane a Kanya
  • Rahoto ya nuna cewa jami'an tsaron dake tare da shi sun yi batakashi da maharan, kuma ɗan sanda mai mukamin ASP ya rasu
  • Sakataren hulɗa da jama'a na mataimakin gwamnan yace Allah ya tseratar da maigidansa amma ya rasa mutum ɗaya

Kebbi - Tsagerun yan bindiga sun farmaki jerin gwanon motocin mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Samaila Yombe, ranar Talata da daddare.

Vanguard ta tattaro cewa yan ta'addan sun kai wa tawagar mataimakin gwamnan hari ne tsakiyar kauyen Kanya da misalin ƙarfe 8:00 na dare.

Yan bindiga
Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kai wa Matimakin Gwamna hari a kan hanya Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A cewar sakataren watsa labarai na mataimakin gwamnan, Abdullahi Yalmo, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce jami'in ɗan sanda ASP Idris Umar Libata, ya rasa rayuwarsa.

Ya ce ɗan sandan ya rasa rayuwarsa ne yayin da suka tarbi yan bindigan, suka yi musayar wuta tsakanin su.

Daga ina mataimakin gwamnan ya fito?

Yalmo ya yi bayanin cewa uban gidanasa tare da rakiyar kwamandan barikin sojojin Najeriya dake Zuru na kan hanyar zuwa ta'aziyya da jaje ga iyalan mutanen kauyen na Kanya.

Mataimakin gwamnan yaje ta'aziyya ne biyo bayan wani mummunan lamarin da ya faru da harin yan bindiga, wanda ya lakume rayukan aƙalla yan Bijilanti 68, da kuma wasu fararen hula da dama.

Sakataren watsa labaran mataimakin gwamnan yace:

"Allah ya tseratar da Uban gidan mu, amma bisa rashin sa'a ya yi rashin ɗaya daga ciki haziƙan yan sandan dake tare da shi."

Da aka tuntubi kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Kebbi, SP Nafiu Abubakar, bai ɗaga kiran wayar da aka jera masa ba domin tabbatar da abin da ya auku.

Yadda lamarin ya faru

Labaran Magaji, ɗan asalin garin Danko Wasagu, ya shaida wa jaridar Premium Times cewa yan bindiga sun farmaki kauyen Kanya tun ƙarfe 5:00 na yamma.

Ya ce:

"Sun ci karfin jami'an tsaron, saboda sun yi gumurzu tun karfe 5:00 na yamma har zuwa karfe 8:00 na dare. Ikon Allah kawai ya tseratar da mataimakin gwamnan, yayin da jami'an tsaro suka tsaya kokarin dakile harin."
"In banda wasu dakarun sojoji da suka kawo ɗauki, da yan bindigan sun ci karfin kowa sun kashe mataimakin gwamnan."

Ya ƙara da cewa bayan yan bindigan sun tafi ne karin sojoji suka iso suka bi bayan su, yayin da wasu kuma suka kwashe gawarwakin waɗan da suka rasu.

A cewar Magaji, sojoji 13 da kuma yan sanda shida dake cikin tawagar mataimakin gwamna ne suka rasa rayuwarsu.

A wani labarin na daban kuma Rikici ya barke tsakanin yan bindiga a Katsina, shugaba ya bindige yaransa har Lahira

Yan sanda sun fara bincike kan kashe wani bawan Allah da yan bindiga suka yi a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Rahoto ya nuna cewa rashin bin umarnin yan ta'addan ya haddasa rikici tsakaninsu, nan take shugaba ya harbe yaronsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel