Da dumi-dumi: Tsohon dan wasan kwallon Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce a Jos

Da dumi-dumi: Tsohon dan wasan kwallon Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce a Jos

  • Tsohon dan wasan Super Eagles, Justice Christopher, ya rigamu gidan gaskiya
  • Christopher ya yanki jiki ne ya fadi a otal din sa dake Gwolshe, wajen Tudunwada Ring road, Jos
  • Lamarin ya afku ne safiyar yau Laraba, 9 ga watan Maris

Plateau - Daily Trust ta rahoto cewa tsohon dan wasan kwallon kafa na Najeriya wato Super Eagles, Justice Christopher, ya mutu.

Jaridar The Guardian ta rahoto cewa tsohon dan wasan tsakiyan ya fadi ne a otal din sa dake Gwolshe, wajen Tudunwada Ring road, Jos da sanyin safiyar Laraba, 9 ga watan Maris.

Daily Trust ta tattaro daga makusantan tsohon dan wasan cewa yana ta fama da cutar hawan jini wanda bai yi tsanani ba.

Da dumi-dumi: Tsohon dan wasan kwallon Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce a Jos
Da dumi-dumi: Tsohon dan wasan kwallon Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce a Jos Hoto: The Punch
Asali: UGC

Gani na karshe da aka yiwa marigayin ya kasance a ranar Talata a cikin abokansa cike da koshin lafiya kuma babu wata alama da ke nuna matsananciyar rashin lafiya a tare da shi.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Jami’in ‘Dan Sandan da ya yi bincike kan Abba Kyari ya mutu kwatsam a ofis

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Koda dai rundunar yan sandan Filato bata riga ta tabbatar da mutuwar Tasa ba, an rahoto cewa an kai gawarsa ajiya a asibitin kwararru na Filato.

Wata majiya ta ce ana sanya ran za a yi gwaji don gano abun da ya kashe shi a asibitin kafin a binne shi.

Jami’in ‘Dan Sandan da ya yi bincike kan Abba Kyari ya mutu kwatsam a ofis

A wani labarin, Joseph Egbunike, wanda shi ne Mataimakin Sufeta-Janar mai kula da sashen FCID na rundunar ‘yan sandan Najeriya ya kwanta dama.

Rahoton da ya fito daga Punch a ranar Laraba, 9 ga watan Maris 2022 ya tabbatar da wannan labari.

Kamar yadda mu ka ji, DIG Joseph Egbunike ya fadi ne cikin ofishinsa a yammacin ranar Talata. Tun daga nan bai farfado ba, sai dai aka dauki gawarsa.

Kara karanta wannan

An tasa keyar dan adawan Ganduje, Dan Bilki Kwamanda, gidan gyara hali

Asali: Legit.ng

Online view pixel