Kotu ta sa ranar fara sauraron bukatar Gwamnatin Buhari na mika Abba Kyari Amurka

Kotu ta sa ranar fara sauraron bukatar Gwamnatin Buhari na mika Abba Kyari Amurka

  • Kotun tarayya dake zaune a Abuja ta sanya ranar 23 ga watan Maris, 2022 domin fara zaman duba bukatar mika Abba Kyari Amurka
  • Gwamnatin Najeriya ta nemi sahalewar Kotu a wani bangare na amincewarta da bukatar mika Kyari ga kasar Amurka
  • Amurka na zargin Kyari da hannu a wata damfara, kuma ta bukaci gwamnatin Buhari ta mika mata shi tun a baya

Abuja - Babbar Kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta zaɓi ranar 23 ga watan Maris, 2022 domin fara tafka mahawara kan bukatar gwamnatin tarayya na miƙa Abba Kyari zuwa Amurka.

Vanguard ta tattaro cewa gwamnatin tarayya ta ofishin Antoni Janar na ƙasa, Abubakar Malami, ta shigar da bukatar gaban Kotu, ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/249/2022.

Karar wacce aka raɗa wa, "Neman sahalewar miƙa Abba Kyari ga ƙasar Amurka," na ɗauke da kwanan wata dai-dai da ranar da aka shigar da ita 2 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Sai irin su Buhari: Osinbajo ya bayyana wanda iya zai magance matsalar tsaro a Najeriya

DCP Abba Kyari
Kotu ta sa ranar fara sauraron bukatar Gwamnatin Buhari na mika Abba Kyari Amurka Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Haka nan kuma, Antoni Janar shi ne wanda ya shigar ƙarar, yayin da mataimakin kwamishinan yan sanda da aka dakatar, Abba Kyari, ne ake neman umarnin Kotun a kansa.

Kyari, ya kasance tsohon shugaban rundunar fasaha ta musamman IRT na Sufetan yan sanda na ƙasa.

Shugaban majlisar Alkalan babbar Kotun tarayya, Mai Shari'a John Tsoho, ya naɗa Mai Shari'a Inyang Ekwo, ya jagoranci shari'ar, kuma an saka ranar 23 ga watan Maris domin fara wa.

An shigar da bukatar ne karkashin dokar miƙa dan ƙasa a wani bangare na amincewar da gwamnatin Najeriya ta yi wa bukatar Amurka na miƙa mata Abba Kyari.

Gwamnati ta tura bukatar ne kai tsaye ga shugaban Alkalai, tare da masa bayanin cewa bukatar ta hito ne daga ofishin diflimasiyya na ofishin jakadancin Amurka a Abuja.

Kara karanta wannan

Farin Jakada: Jarumin Kannywood Ahmad Lawan ya fito takarar siyasa a jihar Katsina

Ƙasar Amurka ta bukaci gwamnatin Najeriya ta miƙa mata Abba Kyari ne domin ya mata karin bayani kan tuhumomin da take da su a a kansa da suka shafi damfara.

APC da mika kujerar shugabanta Arewa ta tsakiya

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ta mika kujerar shugabanta na ƙasa yankin Arewa ta tsakiya

Jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan, ta fitar da jadawalin rarraba ofisoshin shugabanninta zuwa yanki-yanki yayin da ranar babban gangamin taro na kasa ke kara matsowa.

A jadawalin da APC ta fitar yau Laraba a Abuja, jam'iyyar ta miƙa ofishin shugaban jam'iyya na ƙasa zuwa yankin arewa ta tsakiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel