Latest
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kwakwara yabo da addu'o'i ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo bayan cika shekaru 68 a duniya.
Gwamnatin tarayya ta amince da gina matatun mai uku da za su kara yawan gangar man da ake tace zuwa 140,000 a kullum, domin bunkasa samar da mai a Najeriya.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta samu nasarar cafke wasu mutane hudu da ake zargin 'yan bindiga ne. 'Yan sandan sun kwato kayayyaki masu yawa a hannunsu.
Shahararren jarumin fina-finan Kannywood, Abubakar Waziri ya ce da ba ya harkar fim, da ya zama malamin addini saboda yana da sha’awar gyaran al’umma.
Majalisar dattawan Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa an dakatar da Sannata Natasha Akpoti-Uduaghan ne saboda ta zargi Godswill Akpabio da ci mata zarafi.
Bayan kama tsohon gwamnan Akwa Ibom, Gwamnan jihar, Umo Eno, ya nesanta gwamnatinsa daga zargin rashawa na ₦700bn da EFCC ke yi wa Udom Emmanuel.
Idan ana zancen manyan makarantu na jami'a a duniya, ba a maganar na Najeriya. Akwai jami'o'i a Afrika da suke abin yabo da ya kamata a yi koyi da su a nan.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya fadi rawar da marigayi Abba Kyari ya taka wurin cire Joy Nunieh daga mukamin shugabar rikon kwarya a hukumar NDDC.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa yana shirin barin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.
Masu zafi
Samu kari