Latest
Wasu Magoya-bayan Goodluck Jonathan a karkasin wata kungiya mai suna Citizens Network For Peace and Development in Nigeria tana goyon bayan Bola Tinubu a 2023.
Hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA, sun damke wata mata mai shekaru 56 dauke da hodar Iblis kan hanyarta ta zuwa garin Makka dake Saudi Arabia.
Rabiu Musa Kwankwaso ya je Legas, a nan ya raba kan Kungiyar Yarbawa, wasu sun yi wa NNPP mubaya’a bayan sun yi irin haka ga Bola Tinubu da Peter Obi a baya.
Jarumar Kannnywood, Halima Atete, ya shirya tsaf zata Amarce a ranar 26 ga watan Nuwamban wannan shekarar. Tuni da hotunanta da angonta suka bayyana da birgewa.
A karshen makon jiya, Malam Sanusi Lamido Sanusi ya yi jawabi a kan shugabanci a wani taron maulidin Annabi SAW a Abuja, ya yi bayanin wanda za a zaba a 2023.
Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, yace bisa la'akari da zahin abinda ake gani, Bola Tinubu ya cinye zaɓen Kano tun yanzu, zai ci Najeriya a 2023.
A zaman babbar kotun jihar Kano game da shari'ar kisan Ummita, jami'in hukumar 'yan sanda ya ba da shaidar yadda Cheng ya kashe wa Ummita kud'i masu nauyi.
Labarin da muke samu ya bayyana cewa, an samu nasarar yin kaca-kaca da gidan wani dan ta'addan da ke samarwa su Bello Turji makamai a Arewa masu Yammacin kasa.
A rana ɗaya kuma a jiha Ɗaya watau jihar Delta, Bola Tinubu da Peter Obi sun sha mamaki yayin da mutane suka nuna musu ana tare wuraren gangami daban-daban.
Masu zafi
Samu kari