Afenifere: Kwankwaso Ya Je Legas, Kungiyar Yarbawa Ta Dare, Wasu Sun Yi Masa Mubaya’a

Afenifere: Kwankwaso Ya Je Legas, Kungiyar Yarbawa Ta Dare, Wasu Sun Yi Masa Mubaya’a

  • An samu bayyanar ‘Yan kungiyar New Afenifere bayan zuwan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Legas
  • ‘Yan tawaren na Afenifere sun nuna Rabiu Musa Kwankwaso za su bi a 2023 ba Bola Tinubu ko Peter Obi ba
  • Ajibade Adeyeye ya kawo dalilinsu na goyon bayan ‘dan takaran jam’iyyar NNPP a maimakon APC ko LP

Lagos - An samu baraka a tafiyar kungiyar nan ta Afenifere mai kare hakkin Yarbawa. Daily Trust ta fitar da rahoton a karshen makon jiya.

Wannan ya biyo bayan ziyarar da ‘dan takaran NNPP na shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai zuwa Legas a ranar Lahadi.

‘Ya ‘yan kungiyar New Afenifere sun nuna cewa suna goyon bayan takarar da Rabiu Kwankwaso yake yi a karkashin jam’iyyar hamayya ta 2023.

Kwamacala a Afenifere

Kara karanta wannan

Wike da Sauran Gwamnonin G-5 Sun Kafa Sabuwar Kungiya, Sun Ce Sam Ba Zasu Taya Atiku Kamfen Ba

Rahoton yace sabanin da aka samu a kungiyar ta Afenifere ta bayyana a fili bayan kwanakin baya tace tana goyon bayan Asiwaju Bola Tinubu.

Kafin ‘yan kungiyar suce suna tare da ‘dan takaran na APC, Pa Ayo Adebanjo wanda yake jagorantar Afenifere, ya yi wa Peter Obi na LP mubaya’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin da tsohon gwamnan Kano ya kai ziyara zuwa Legas domin bude ofisoshin jam’iyyar NNPP, sai ga shi ya samu goyon bayan New Afenifere.

Rabiu Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso a Ikoyi Hoto: @mohd.saifullahi.9
Asali: Facebook

Dalilin goyon bayan Kwankwaso - Adeyeye

Jagoran New Afenifere na kasa, Kwamred Ajibade Adeyeye yace sun yi wa Kwankwaso mubaya’a ne saboda ganin irin ayyukan da ya yi a baya.

"A madadin New Afenifere, mun amince za mu goyi-bayan takarar Rabiu Musa Kwankwaso da Bishof Isaac Idahosa domin ganin sabuwar Najeriya
Muna kira ga dattawan mu da su daina kakaba mani 'dan takara, su kyale mu, mu tsaida ‘dan takaran shugaban kasarmu, domin mun san ciwon kanmu."

Kara karanta wannan

Magoya Baya da Makusantan Jonathan Sun Yanke Shawara, Sun Faɗi Wanda Suke So Ya Gaji Buhari a 2023

- Ajibade Adeyeye

Kwankwaso ya karbi mubaya'a

Vanguard tace ‘dan takaran ya karbi wannan mubaya’a da aka yi masa, ya yi alkawarin zai yi tafiya da kowa a gwamnatinsa, idan NNPP ta ci zabe.

Kwankwaso yace bai yi mamakin goyon bayan da ya samu ba domin akwai matasa da-dama da ke tare da shi, kuma dama tafiyarsu ta matasa da mata ce.

Wa za a zaba - Sanusi II

An ji labari Gidauniyar Ashraaf Islamic Foundation ta shirya bikin Maulidin Annabi Muhammad SAW, aka kira Sanusi Lamido Sanusi ya gabatar da jawabi.

Khalifan Tijjaniya na Najeriya ya bayyana cewa ana bukatar Musulmai a kan mulki, kuma ya yi bayanin abubuwan da ake bukata daga wanda zai yi jagoraci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel