Labarin Usama Yarima, matashi dan a mutun Buhari da ya kwana a dakin da babu hotun shugaban kasa

Labarin Usama Yarima, matashi dan a mutun Buhari da ya kwana a dakin da babu hotun shugaban kasa

  • Dan a mutun Buhari ya bayyana irin kaunar da yake yiwa Buhari, ya ce sam ba ya kwana a dakin da babu hoton Buhari
  • Ya kuma bayyana baiwar da Allah ya yi masa na haddace kananan hukumomin Najeriya duk da bai taba zuwa makaranta ba, yana son yin karatu babu dama
  • A wani bangare kuma, mutumin da ya yanka raguna saboda soyayyar Buhari ya saki APC, ya koma tsagin su Kwankwaso

Jihar Jigawa - Wani matashi dan a mutun Buhari ya bayyana yadda soyayyar Buhari ta shajja'a shi ya koyi karatun Boko duk da kuwa bai taba shiga aji ba.

A wani bidiyon da BBC Hausa ta yada na hira da Usama Yarima, an ga lokacin da yake share kura a hotunan shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya manna a dakinsa, tare da bayyana kaunarsa gareshi.

Kara karanta wannan

Na Daina Karatun Soshiyal Midiya Saboda Yana Sa Jinina Yana Hawa, Tinubu

Usama dai dan yankin Kazaure ne a jihar Jigawa, kuma ya ce shi da ne ga Yariman Kazaure.

Ya ce bai da burin da ya wuce a yanzu ya yi karatu, kuma rashin abinci ne ya hana shi fara karatu, ya roki a taimaka masa ya cika burinsa.

Dan a mutun Buhari ya ba da labarinsa
Labarin Usama Yarima, matashi dan a mutun Buhari da ya kwana a dakin da babu hotun shugaban kasa | Hoto: BBC Hausa/Mujalla
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, Usama ya bayyana cewa, a yanzu dai yana iya karanta jarida duk da kuwa bai da tarihin shiga makaranta, duk sanadiyyar Buhari.

Ya haddace kananan hukumomi 744 na Najeriya

A bangare guda, ya bayyana baiwar da Allah ya yi masa na kaifin haddace jerin kananan hukumomin Najeriya gaba dayansu, inda a bidiyon ya yi baje-kolin baiwarsa ta hanyar lissafa sunayen wasu.

Legit.ng Hausa ta lura da yadda Usama ya lissafa kananan hukumomin jihar Borno 27 ba tare da bata ba, kana ya kawo na jihar Kuros Riba 18.

Kara karanta wannan

Na Fasa: Ana Gab Da Daurin Aure, Ango Yace Ya Fasa Bayan Gano Amaryar Na Da 'Yaya 2

A bangare guda, ya haddace kananan hukumomin ta hanyar sanin bakaken rubutu, inda yake dasa kowane baki da adadin kananan hukumomin da yake wakilta a fadin kasar, kamar yadda ya shaidawa BBC Hausa.

Kalli bidiyon:

Dan a mutun Buhari ya koma jam'iyyar su Kwankwaso mai kayan marmari

Alhaji Abubakar Rabiu, wani masoyin Buhari ya bayyana sauya sheka zuwa jam'iyyar NNPP ta su Kwankwaso duk kuwa da son sa da APC a baya.

A shekarun da suka gabata ne Rabiu ya kwantar da rago sukutum ya yanka a murnar dawowar shugaban kasa Buhari daga kasar waje a doguwar jinyar da ya yi.

Al'adarsa ce yanka raguna duk lokacin da shugaban ya dawo daga kasar waje, rahotanni sun ce ya yi hakan akalla sau takwas kafin daga bisani ya yiwa APC saki uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel