Kwamandojin Boko Haram 2 da Wasu Mayaka 47 Sun Tuba, Sun Mika Wuya ga Soji

Kwamandojin Boko Haram 2 da Wasu Mayaka 47 Sun Tuba, Sun Mika Wuya ga Soji

  • ’Yan ta’adda 49 na kungiyar ta’addancin Boko Haram ne suka mika wuya ga dakarun sojin Najeriya dake garin Damboa a jihar Borno
  • Kamar yadda aka gano, kwamandojin kungiyar biyu, Baa Usman da Alhaji Ari, suna daga cikin wadanda suka mika wuya ga dakarun a ranar 20 ga Nuwamba
  • Binciken farko ya nuna cewa, ‘yan ta’addan sun fito ne daga dajin Sambisa inda suka dade a boye suna hada makircin yaki

Borno - A kalla mayakan ta’addanci 49 na kungiyar Jama’at Ahl Sunnah Lid da’awah wal jihad wadanda aka fi sani da Boko Haram ne suka mika wuya.

Tubabbun ‘yan ta’adda
Kwamandojin Boko Haram 2 da Wasu Mayaka 47 Sun Tuba, Sun Mika Wuya ga Soji. Hoto daga @ZagazOlamakama
Asali: Twitter

Daga cikin ‘yan ta’addan har da manyan kwamandojin biyu masu suna Ba’a Usman (Munzir) da Alhaji Ari (Nakib) duk sun mika wuya ga dakarun sojin Najeriya.

Wata majiyar ta tsaro ta sanar da Zagazola Makama, kwararre a fannin kiyasin tsaro da yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi, cewa ‘yan ta’addan sun mika wuya ne a ranar 20 ga watan Nuwamban 2022 ga rundunar Operation Hadin Kai a garin Damboa.

Kara karanta wannan

Duk Wanda Yace 2023 Lokacinsa ne, Ya Tafka Babban Kuskure, Kwankwaso Yayi Gugar Zana

Kamar yadda Zagazola Makama suka wallafa a Twitter, binciken farko ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun fito ne daga dajin Sambisa inda suke boye tare da kulla duk wasu makircin yaki da hana zaman lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sama da ‘yan ta’adda 90,00 sun mika wuya ga sojoji

Idan za a tuna, a kalla ‘yan ta’adda 90,000 da suka hada da masu yaki da wadanda basu zuwa fagen fama da iyalansu ne suka mika kai ga rundunar sojin Najeriya.

Majiyoyi sun ce tsanantar yakarsu da dakarun sojin ke yi yana daga cikin dalilin da yasa suke ta mika wuya.

Tubabbun ‘yan ta’adda sun tsaftace Maiduguri, sun roki yafiya

A wani labari na daban, wasu tubabbun ‘yan ta’addan Boko Haram sun yi aikin tsaftace babban birnin jihar Borno, Maiduguri.

Cibiyar damokaradiyya ta CDD tare da hadin guiwar gwamnatin jihar Borno ce ta shirya.

A yayin sharar, wasu cikinsu sun saka to riguna masu rubutun neman yafiya da gafara daga jama’ar jihar inda suke bayyana tubansu kuma ba zasu sake ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel