Kyawawan Hotunan Kafin Auren Jaruma Halima Atete da Angonta ‘Dan Kwalisa

Kyawawan Hotunan Kafin Auren Jaruma Halima Atete da Angonta ‘Dan Kwalisa

  • Fitacciyar jarumar Kannywood, Halima Atete, ta shirya tsaf domin amarcewa a ranar 26 ga watan Nuwamban 2022 a garin Maiduguri na jihar Borno
  • Kyawawan hotunan amaryar tare da angonta mai suna Mohammed Mohammed Kala sun bayyana cike da birgewa tare da kwalisa
  • Tuni jama’a suka dinga tururuwar taya jarumar murna tare da yi mata fatan alkhairi yayin da take shirin cike rabin addininta

Maiduguri, Borno - Aure yakin mata in ji Hausawa. Hakan kuwa yake domin a duk lokacin da Allah ya nufa lokacin auren mace ya yi, ko babu shiri za a yi shi.

Jaruma Halima Atete
Kyawawan Hotunan Kafin Auren Jaruma Halima Atete da Angonta ‘Dan Kwalisa. Hoto daga BBC Hausa
Asali: Facebook

Wannan shekarar matan masana’antar Kannywood Allah ya tarfawa garinsu nono inda daya bayan daya suke ta shigewa dakunan mazajensu.

Bayan mako biyu kacal da auren Rukayya Umar Santa wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya, Allah ya yarda jaruma Halima Atete zata bi bayanta inda ita ma zata shige gidan aure.

Kara karanta wannan

Kano: A Zaman Kotu, An Gano Dalilin da Yasa Ɗan China Ya Ba Ummita Kyautar Miliyan N18m da Sabon Gida

Kamar yadda aka sani, jarumar ‘yar asalin jihar Borno ce kuma tayi shuhura a masana’antar Kannywood sakamakon kwarewarta a wasan kwaikwayon.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A ranar 26 ga watan Nuwamban 2022 za a daura auren jarumar da angonta ‘dan kwalisa mai suna Mohammed Mohammed Kala a garin Maiduguri dake jihar Borno.

A cikin kyawawan hotunan kafin auren da suka bayyana, jarumar ta ci ado cikin shigar lafaya sannan da kwalliyar mata masu ji da kasaita.

Ango Mohammed Kala ma ba a bar shi a baya ba, ya fito fes cikin shigar manyan kaya na riga da wandon shadda har da hula wanda ta dace da shi.

Jama’a sun yi martani

Nazif Abubakar yace:

”Ina taya ma’auratan murna amma tunatarwa. A Musulunci an haramtawa jiki biyu su hadu kafin a tabbatar da daurin aure. Haduwar jiki a nan ana nufin taba juna.”

Kara karanta wannan

Kwana 1 Da Yin Wa'azin Mutuwa Bayan Cikarsa Shekaru 40, Allah Ya Yiwa Wani Matashin Gombe Cikawa

Ashiru Hamza:

”Allah yasa alkhairi, sauran da ba su yi ba Allah ya karkato da hankalin su suma su san cewa zama dakin mijin su ya fiye masu wannan shirin film din.”

Abdul M Inuwa:

”Hannun mutumin bayan aiki ne kuma? Fatan alkhairi.”

Mustapha Meena Kaura Goje :

“Rahama, Nafisa, Maryam Booth, Fati Washa da sauransu, ana magana.”

Nuraddeen Abdullahi ‘Yar Maiwa:

”Allah ya sa albarka a cikin wannan aure ya ba su zuri'a ɗayyiba.”

Muhammad Ahmad:

”Allah Ubangiji yasa hakan ya tabbata. Gaskiya nayi murnan jin hakan. Wallahi sai naji kamar ’yar uwata wallah. Allah yasa a yi a sa’a.”

Rukayya Dawayya da Afakallahu sun yi aure

A cikin ‘yan makonnin da suka gabata ne aka daura auren jaruma Rukayya Dawayya da Isma’il Na’Abba Afakallahu a garin Kano.

’Yan uwa, abokan arziki da abokan sana’arta na fim duk sun garzaya wurin taya ta murna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel