2023: Hotunan Yadda Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu Suka Tara Jama'a a Jiha Daya

2023: Hotunan Yadda Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu Suka Tara Jama'a a Jiha Daya

  • Biyu daga cikin manyan yan takarar dake sahun gaba sun gudanar da gangamin yakin neman zaɓe a jihar Delta
  • Bola Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki da takwaransa na jam'iyyar LP, Peter Obi sun samu kyakkyawar tarba daga tulin jama'a a wurare daban-daban
  • Yakin neman zaɓen kujera lamba ɗaya a Najeriya ya kankama a kusan dukkanin manyan jam'iyyu yayin da zaben 2023 ke ƙara matso wa

Delta - Mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, da takwaransa na jam'iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu, sun tara dandazon jama'a a wurare mabanbanta ranar Asabar a jihar Delta.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jama'a sun yi cikar kwari yayin da suka yi marhabun da Peter Obi a sansanin Charismatic Renewal da ke Ubulu Uku a jihar.

Kara karanta wannan

Ana Tsaka da Shan Soyayya, Budurwa Ta Burma Wa Saurayinta Sadiq Ɗahiru Wuka Har Lahira

Haka zalika jama'a sun cika ko ina ba masaka tsinke a wurin gangamin jam'iyyar APC na Bola Tinubu a babban filin wasan Warri Township duk a jihar Delta, kudu maso kudancin Najeriya.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa baki ɗaya wurare biyun da 'yan takarar suka gudanar da yaƙin neman zaɓensu ya cika maƙil da mutane kamar yadda zaku gani a Hotuna.

Wurin gangamin Bola Tinubu

Tinubu a Delta.
2023: Hotunan Yadda Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu Suka Tara Jama'a a Jiha Daya Hoto: dailytrust
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron Tinubu a Delta.
2023: Hotunan Yadda Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu Suka Tara Jama'a a Jiha Daya Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Taron APC a Delta.
2023: Hotunan Yadda Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu Suka Tara Jama'a a Jiha Daya Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Gangamin Tinubu a Delta.
2023: Hotunan Yadda Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu Suka Tara Jama'a a Jiha Daya Hoto: Dailytrust
Asali: UGC

Taron Peter Obi

Peter Obi.
2023: Hotunan Yadda Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu Suka Tara Jama'a a Jiha Daya Hoto: Dailytrust
Asali: UGC

Gangamin Peter Obi.
2023: Hotunan Yadda Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu Suka Tara Jama'a a Jiha Daya Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Peter Obi.
2023: Hotunan Yadda Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu Suka Tara Jama'a a Jiha Daya Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa yayin da zaɓe ya rage watannin da basu wuce uku ba, kowane ɗan takara ya matsa kaimi wajen tallata takararsa ga 'yan Najeriya.

Tinubu na APC, Atiku na jam'iyyar PDP, Peter Obi na jam'iyyar LP, da Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP ne ake ganin su a sahun gaba wajen damar lashe zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Magoya Baya da Makusantan Jonathan Sun Yanke Shawara, Sun Faɗi Wanda Suke So Ya Gaji Buhari a 2023

A wani labarin kuma Magoya Baya da Makusantan Jonathan Sun Yanke Shawarar mara wa Bola Tinubu Baya ya gaji Buhari a 2023

Fitacciyar ƙungiyar da ta yi bakin kokarinta wurin ganin Jonathan ya nemi takara a APC, ta jaddada matsayar cewa ya zama tilas mulki ya koma kudu.

Ƙungiyar Citizens Network For Peace and Development in Nigeria (CNPDN) tace bayan nazari da neman shawari, sun cimma matsayar tsaya wa bayan Tinubu na jam'iyyarAPC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel