Gwamna Wike Ya Karbi Bakunci Kwankwaso Domin Kaddamar da Wani Aiki A Ribas

Gwamna Wike Ya Karbi Bakunci Kwankwaso Domin Kaddamar da Wani Aiki A Ribas

  • Mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya isa Patakwal, babban birnin Ribas
  • Tsohon gwamnan Kanon ya samu maraba daga gwamna Nyesom Wike yayin da yake shirin kaddamar da wani aiki
  • Gwamna Wike ya gayyaci manyan yan siyasa daga jam'iyyun adawa suna kaddamar da ayyukansa yayin da rigima ta addabi PDP

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya karbi bakuncin ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar NNPP mai kayan daɗi, Rabiu Musa Kwankwaso, a Patakwal.

Kwankwaso ya kai ziyara Ribas ne domin amsa gayyatar da Wike ya masa na zuwa kaddamar da Titunan cikin garin Mgbutanwo, ƙaramar hukumar Emohua ranar Litinin.

Gwamna Wike tare da Kwankwaso.
Gwamna Wike Ya Karbi Bakunci Kwankwaso Domin Kaddamar da Wani Aiki A Ribas Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan Kano, Kwankwaso, ne ya sanar da isarsa Patakwal a wani rubutu da ya saki a shafinsa na dandalin Tuwita.

Kara karanta wannan

Mai Bakin Cin Rashawa Bai Isa ya Jagoranci Kamfen ba, Wike ga Shugaban PDP

Wike ya gayyaci manyan jiga-jigan siyasa na jam'iyyun adawa daban-daban domin su kaddamar da manyan ayyukan gwamnatinsa a jiha mai tarin albarkatun man Fetur dake kudu maso kudu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnan yace yana gayyyato 'yan siyasan jam'iyyun adawa ne domin su gane wa idonsu sannan su koma su faɗa wa mutanensu.

Yan siyasan da Wike ya gayyata

A ranar Laraba data shuɗe, tsohon shugaban APC na ƙasa, Adams Oshiomhole, ya kaddamar da gadar sama ta 8 a titin Ada George gefen gidan Wike na kai da kai a mahaifarsa, Rumueprikom, ƙaramar hukumar Obio-Akpor.

Haka zalika ɗan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya kaddamar da Gadar Sama ta 9 a fitacciyar mahaɗar hanyoyi dake Ikoku ranar Alhamis.

Bugu da ƙari, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kaddamar da reshen makarantar koyon aikin Lauya ta Najeriya a Patakwal ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Wike Ya Sake Tada Kura, Ya Ce PDP Za Ta Gane 'Khaki Ba Leda Bane'

Rigingimun jam'iyyar PDP

A yan watannin da suka gabata, Gwamna Wike tare da wasu gwamnoni huɗu da ake kira Gt sun nemi Iyorchia Ayu ya yi murabus. A cewarsa bai dace arewa ta haɗa shugaban PDP na ƙasa da tikitin shugaban ƙasa ba.

A ɓangarensa, Ayu ya kafe cewa ba zai sauka daga mukaminsa ba har sai wa'adin mulkinsa na shekaru hudu ya cika duk da G5 sun ce sai ya sauka zasu mara wa Atiku baya.

Har yanzun Wike da mutanensu ba su halarci ko ɗaya daga tarukan Kamfen Atiku ba, kuma babu tabbacin wa zasu mara wa baya tsakanin Tinubu da Peter Obi a 2023.

A wani labarin kuma Bola Tinubu da Peter Obi sun gudanar da gangamin kamfe a jihar Delta ɗana ɗaya watau ranar Asabar

Wasu Hotuna da muka tattara muku sun nuna yadda wuraren gangamin APC da LP suka cika suka batse da jama'a a jihar da abokin takarar Atiku ke jagoranta

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Wasu Gwamnoni Sun Kama Hanyar Ficewa Daga PDP? Atiku Ya Yi Magana

Magoya bayan APC sun yi cincirindo don nuna wa Tinubu ƙauna kamar yadda mambobin LP suka yi dafifi don tarban ɗan takarar jam'iyyarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel