Latest
Ɗan takarar kujerar sanatan Kano ta Kudu na jam'iyyar NNPP, Kawu Sumaila, ya.lallasa sanata Kabiru Gaya na jam'iyyar APC, a ƙaramar hukumar sa ta Gaya a Jihar.
Za a ji Jam’iyyar LP ta karbe kujerar ‘dan majalisar wakilan tarayya na shiyyar Kaura a jihar Kaduna. Donatus Mathew wanda ya taba zama ‘Dan acaba ya ci zabe.
Yanzu muke samun labarin cewa, tsohon gwamnan jihar Edo ya yi nasara a zaben sanata da aka gudanar a mazabarsa, inda ya banke abokin hamayyarsa na yankin a PDP.
Ƙawo yanzun da aka ayyana sakamakon zaben shugaban kasa daga kananan hukumomi 17 cikin 20 na jihar Legas, Peter Obi na LP na kan gaban Bola Tinubu na APC .
Shugaban majalisar datawa, Ahmed Lawan, ya sake lashe zabe a matsayin sanata mai wakiltan Yobe ta Arewa. INEC ta sanar da haka bayan ya lallasa dan takarar PDP.
Sanata Abdullahi Adamu, Shugaban jam'iyyar APC na kasa ya gaza kawo wa jam'iyyarsa ta APC kujerar sanata na yankin Nasarawa ta Yamma a zaben ranar Asabar 25.
Gwamna Ben Ayade na jihar Cross River da takwaransa Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu sun sha kaye a zaben sanata da aka yi a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.
Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya bada umurnin haramta duk wani nau'in zanga-zanga a jiharsa. Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida da tsaro ya sanar.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a jihar Katsina. Atiku ya samu ƙuri'u fiye da Tinubu na APC a jihar.
Masu zafi
Samu kari