Tsohon Gwamna Oshiomhole Ya Lashe Zaben Sanatan Edo Ta Arewa

Tsohon Gwamna Oshiomhole Ya Lashe Zaben Sanatan Edo Ta Arewa

  • Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa ya lashe zaben sanata a mazabar Edo ta Arewa a Kudancin Najeriya
  • Adams Oshiomole ya samu kuri'u da yawa, inda ya banke abokan hamayyarsa a jam'iyyar PDP da sauran jam'iyyu
  • Ana ci gaba da fito da sakamakon zabe a yankuna daban-daban na Najeriya tun bayan kammala zabe a ranar Asabar

Jihar Edo - Adams Oshiomole, tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa ya lashe kujerar sanata a Edo ta Arewa

Oshionole ya samu kuri'u 107,110, inda ya banke abokin hamayyarsa Francis Alimikhena na jam'iyyar PDP, Sahara Reporters ta tattaro.

Alimikhena ya samu kuri'u 55,344.

Edo ta yi sabon sanata, Oshiomole
Tasiwar jihar Edo | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Hukumar INEC ta sanar da Oshiomole ne ya lashe zabe

Benjamin Adesina, baturen zabe a jihar Edo ya sanar da cewa, dan takarar da ya lashe zabe a mazabar Edo ta Arewa dai ba kowa bane face Oshiomole.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Obasanjo Ya Nemi a Soke Zaben Shugaban Kasa Na 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Adams Oshiomole na APC, ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben, don haka shi ne dan takarar da ya lashe zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Faburairu a mazabar sanata ta Edo ta Arewa.

Adams Oshiomole ya kasance daya daga cikin masu fada a ji a jam'iyyar APC mai mulki, kuma ya yi gwamna a Edo a shekarun baya da suka shude.

A lokacin da yake shugaban APC ne aka kafa gwamnatin Buhari, kuma tasirinsa ya shafi bangarori daban-daban na siyasar jam'iyyar.

Sanata Bala Ibn Na'Allah ya rasa kujerarsa ta sanata

A wani labarin kuma, jigon APC mai fada a ji ya rasa damar zama sanata a zaben 2023 na 'yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata 25 ga watan Faburairu.

Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, dan takarar sanata a PDP ne ya yi nasarar karbe kujerar a hannun Sanata Bala, wanda ya dade yana rike da ita.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Lashe Zabe a Jihar Oyo, Ya Doke Atiku Da Kuri’u Masu Yawan Gaske

A cewar rahoton, Bala ya kasance sanata har sau biyu a mazabarsa da ke Kebbi, inda kuma ya kasance dan majalisar wakilai a matakin tarayya na tsawon zango biyu a jihar ta Kebbi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel