Kawu Sumaila Ya Lallasa Sanatan APC Mai Ci Yanzu a Ƙaramar Hukumar Sa

Kawu Sumaila Ya Lallasa Sanatan APC Mai Ci Yanzu a Ƙaramar Hukumar Sa

  • Ɗan takarar jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, Kawu Sumaila, lallasa abokin hamayyar sa na jam'iyyar APC
  • Kawu Sumaila yana kan gaba a mafi yawan ƙananan hukumomin da aka kammala bayyana sakamakon su
  • Sanata Kabiru Gaya na jam'iyyar APC, ya shafe tsawon lokaci yana wakilci a majalisar dattawan Najeriya

Kano- Ɗan takarar sanatan Kano ta Kudu na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Hon Abdulrahman Kawu Sumaila, ya lallasa sanata mai ci yanzu Kabiru Ibrahim Gaya, a ƙaramar hukumar sa ta Gaya.

Hakan na ƙunshe ne a cikin sakamakon da hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta sanar a jiya Lahadi. Rahoton Leadership.

Kawu Sumaila
Kawu Sumaila Ya Lallasa Sanatan APC Mai Ci Yanzu a Ƙaramar Hukumar Sa Hoto: Leadership
Asali: UGC

Bayanin sakamakon zaɓen wanda jami'in tattara sakamakon zaɓe, Farfesa Lawal Suleiman Bilbis, ya fitar, ya nuna cewa a ƙaramar hukumar Rogo, akwai yawan masu kaɗa ƙuri'a 112194 inda aka tantance mutum 33,150.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Atiku Ya Kunyata Buhari a Jihar Katsina, Ya Lallasa Tinubu a Jihar

Jam'iyyar APC ta samu ƙuri'u 10,354, NNPP ta samu ƙuri'u 20,242, sai PDP ta samu ƙuri'u 1331.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A ƙaramar hukumar Gaya, jam’iyyar APC ta samu ƙuri’a dubu goma da saba’in da tara (10,079), yayin da jam’iyyar NNPP, ta samu ƙuri’u dubu goma sha takwas da ɗari huɗu da goma sha tara (18,419).

Sannan jam’iyyar PDP ta samu ƙuri’u ɗari bakwai da arba’in da bakwai (747). Rahoton Daily Trust

A ƙaramar hukumar Ajingi, akwai yawan masu kaɗa ƙuri'a 86453, inda aka tantance mutum 27, 776, wanda a ciki jam'iyyar APC ta samu ƙuri'u 7,153, PDP ta samu ƙuri'u 1157 sannan NNPP ta samu ƙuri'u 17,061.

A ƙaramar hukumar Bunkure, akwai yawan masu kaɗa ƙuri'a 97, 059, inda aka tantance mutum 31, 152, wanda a ciki jam'iyyar APC ta samu ƙuri'u 11,057, PDP ta samu ƙuri'u 1026 sannan NNPP ta samu ƙuri'u 17, 437.

Kara karanta wannan

Sakamakon Kano: Kwankwaso Ya Lallasa Bola Tinubu a Karamar Hukumar Gwamna Ganduje

Sakamakon zaɓen a sauran ƙananan hukumomin ya kasance kamar haka, ƙaramar hukumar Albasu, APC – 9718, PDP – 1,192, NNPP – 20,315; ƙaramar hukumar Garko, APC -8,500, PDP – 921, NNPP – 17, 018,.

Ƙaramar hukumar Sumaila, APC -11, 947, PDP – 896 sannan NNPP – 25304

A wani labarin na daban kuma, Atiku Abubakar ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a jihar Katsina.

Ɗan takarar na jam'iyyar PDP ya lallasa abokin hamayyar sa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel