Solomon Dalung Ya Sha Kaye a Mazabarsa, PDP Ta Lashe Zabe

Solomon Dalung Ya Sha Kaye a Mazabarsa, PDP Ta Lashe Zabe

  • Solomon Dalung, tsohon minista a Najeriya ya sha kaye a zaben majalisar dokokin tarayya da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata
  • Mrs Beni Lar ce ta lashe zaben da adadin kuri'u masu yawa, kuma wannan ne karo na biyar da za ta ci gaba da zama a kujerar
  • Dalung, wanda ya tsaya takara a jam'iyyar SDP ya zo na uku a zaben, inda dan takarar APC ya zo na uku

Jihar Filato - Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung ya fadi a zaben majalisar wakilai da aka gudanar a mazabarsa a ranar Asabar.

Dalung ya samu kuri'u 3,369 kacal a matsayinsa na dan takarar jam'iyyar SDP, inda ya zo na uku a jerin 'yan takarar majalisar tarayya a mazabar Langtang North/Langtang South.

Wacce ta lashe zaben, Beni Lar 'yar jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 42,008, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Taliyar karshe: Fitaccen sanata, Na'Allah ya rasa kujerar sanata, dan PDP ya lashe zabe

Dalung ya fadi zabe a Filato
Taswirar jihar Filato, inda Dalung ya fadi zabe | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ba wannan ne farkon lashe zabenta ba

Bayan lashe zaben, Mrs Beni Lar za ta ci gaba da zama 'yar majalisar yankin a karo na biyar kenan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Na biyu a mazabar, Vincent Bulus na jam'iyyar APC mai mulki ya samu kuri'u 21,345.

Dalung dai ya kasance daya daga cikin ministocin da Buhari ya tsige a mulkinsa saboda wasu dalilai.

Bayan haka, ya fita daga APC tare da sukar yadda gwamnatin jam'iyyar ke tafiyar da lamuranta yadda a tunaninsa yace bai dace ba.

Sakamako dai na ci gaba da fitowa, jiga-jigai da yawa a kasar nan sun rasa kujerunsu na siyasa da suka dade suna rike dasu a zaben bana.

Na'Allah ya rasa kujerarsa ta sanatan Kebbi

A wani labarin kuma, sanata Bala Ibn Na'Allah ya ci taliyar karshe a majalisar dattawan Najeriya, dan takarar jam'iyyar PDP ya lashe zaben da aka yi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hawaye, Alhini Yayin Da Dan Majalisar Jihar Kogi Ya Rasu Bayan Zabe

An sanar da cewa, Bala Na'Allah zai zauna a gida na tsawon shekaru bayan da wani sabon dan takarar PDP ya kawo kuri'u mafi rinjaye a zaben na bana.

Na'Allah ya rike mukamin sanatan Kebbi ta har tsawon shekaru 12 kafin a yi waje dashi a wannan zaben na bana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel