Yanzu Yanzu: Tinubu Ya Lashe Zabe a Jihar Oyo, Ya Lashe Gaba Daya Kananan Hukumomi 33

Yanzu Yanzu: Tinubu Ya Lashe Zabe a Jihar Oyo, Ya Lashe Gaba Daya Kananan Hukumomi 33

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na APC ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Oyo kamar yadda INEC ta sanar
  • Tinubu ya samu kuri'u 449,884 a fadin kananan hukumomi 33 na jihar inda ya yi wa sauran abokan hamayyarsa zarra
  • Atiku Abubakar na PDP ya zo na biyu da kuri'u 182,977, Peter Obi na da 99,110 yayin da Sanata Rabiu Kwankwaso na NNPP ke da 4095

Oyo - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar a jihar Oyo kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta sanar.

Tinubu ya lashe zabe a kananan hukumomi 33 na jihar yayin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya zo na biyu, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Assha: Tsohon ministan Buhari, Dalung ya sha kaye a mazabarsa

Asiwaju Bola Tinubu tsaye da dungulen hannu
Yanzu Yanzu: Tinubu Ya Lashe Zabe a Jihar Oyo, Ya Lashe Gaba Daya Kananan Hukumomi 33 Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi,, ya zo na uku a zaben da aka gudanar a fadin jihar.

Yawan kuri'un da kowani dan takara ya samu

Kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto, Tinubu ya samu jimilar kuri'u 449,884, Atiku ya samu kuri'u 182,977, Obi ya tashi da 99,110 yayin da Sanata Rabiu Kwankwaso na NNPP ya samu 4095.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Baturen zabe na kananan hukumomin jihar ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zabe, sakatariyar INEC da ke Agodi, Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar Litinin, 27 ga watan Fabrairu.

Ga wasu daga cikin sakamakon kananan hukumomin a kasa:

Karamar hukumar Ibadan ta arewa maso yamma

APC 13078

PDP 6011

LP 4820

Karamar hukumar Kajola

APC 11917

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Atiku Abubakar Ya Yi Nasara, Ya Lallasa Bola Tinubu a Jihar da APC Ke Mulki

PDP 9358

LP 503

Karamar hukumar Afijio

APC 8876

PDP 4112

LP 1925

Karamar hukumar Itesiwaju

APC 6180

PDP 4948

LP 387

Karamar hukumar Atisbo

APC 7928

PDP 4031

LP 1178

Karamar hukumar Atiba

APC 15046

PDP 6180

LP 1234

Karamar hukumar Lagelu

APC 16011

PDP 5112

LP 4066

Karamar hukumar Oyo ta yamma

APC 14076

PDP 4544

LP 1724

Karamar hukumar Iseyin

APC 19731

PDP 6588

LP 1371

Karamar hukumar Ibarapa ta gabas

APC 10575

PDP 4800

LP 779

Karamar hukumar Saki ta gabas

APC 6414

PDP 3634

LP 1144

Karamar hukumar Ibarapa ta tsakiya

APC 10291

PDP 5169

LP 726

A wani labarin, mun kawo cewa Bola Tinubu na gaba da Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a sakamakon kananan hukumomin jihar Sokoto 10.

Asali: Legit.ng

Online view pixel